'Ba Ruwanmu da ko Kai Wanene,' Babachir Lawal Ya Fadi Wanda Arewa Za Ta Zaba a 2027

'Ba Ruwanmu da ko Kai Wanene,' Babachir Lawal Ya Fadi Wanda Arewa Za Ta Zaba a 2027

  • Babachir Lawal ya bayyana cewa Arewa za ta canza tsarin tantance wanda za ta zaba a 2027 don kaucewa abin da ya faru a 2023
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce Arewa za ta zabi dan takarar da ya fahimci matsalolinta kuma ya shirya magance su
  • Yayin da ya ce shiyyar ba za ta yi la'akari da yare ko tarihin siyasar dan takara ba, Babachir ya ce an kafa sabuwar kungiyar NPCP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce Arewa za ta yi amfani da sababbin matakai na tantance wanda za a zaba a 2027.

Babachir Lawal ya ce ba za a yi amfani da irin matakan da aka bi a 2023 aka zabi shugaban kasa ba, yana mai cewa idan kida ya canja, dole rawa ma ta canza.

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce Arewa za ta zabi wanda ya fahimci matsalolinta ne kawai a 2027
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Buhari, Babachir Lawal. Hoto: @OneJoblessBoy
Asali: Facebook

Tsohon babban jami'in gwamnati a lokacin Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Channels TV a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Wanda Arewa za ta zaba a 2027' - Babachir

Ya bayyana cewa akwai sabon tsarin siyasa da aka amince da shi don amfanin Arewa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

A cikin wannan tsari, ya ce an samar da sabuwar kungiyar 'yan siyasar Arewa wacce za ta mayar a hankali kan hada kan mutane da zaben mutane na-gari.

Babachir Lawal ya ce kungiyar za ta zabi dan siyasar da ya nuna ya fahimci matsalolin yankin, ba tare da la'akari da yare ko tarihin siyasarsa ba.

A wannan gabar ne Babachir Lawal ya ce ba ya jin zai iya mara wa Peter Obi baya a zabe mai zuwa duk da cewa shi tsohon masoyin jam'iyyar LP ne.

Da yake tsokaci kan zaben dan takara a 2027, Babachir Lawal ya ce:

Kara karanta wannan

"Ba Tinubu ba ne," Sakataren Gwamnatin Tarayya a mulkin Buhari ya fadi wanda ya ci zaben 2023

"Abubuwa sun canja. Matakan da aka yi amfani da su a 2023 ba su ne za a yi amfani da su wajen tantance dan takara a 2027 ba"

An kafa sabuwar kungiyar siyasa a Arewa

Da yake magana game da matsayar yankin gabanin zabukan 2027, Babachir Lawal ya ce Arewa za ta zabi mutumin da ya san matsalolinsu kuma yake da niyyar magance su.

Ya ce sabuwar kungiyar 'yan siyasar Arewa wadanda ba sa cikin gwamnati ne suka kirkiri kungiyar NPCP domin hada kan jama'a da magance matsalolin yankin.

Babachir Lawal ya ce kungiyar ta amince cewa Arewa za ta yi zabe ne da murya daya, yana mai cewa idan ba a hada kai ba, to shiyyar ba za ta taba cika burinta ba.

Babachir Lawal ya ce an kafa sabuwar kungiyar 'yan siyasar Arewa don tunkarar zaben 2027
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya fadi shirin Arewa gabanin 2027. Hoto: @OneJoblessBoy
Asali: UGC

"Za a samar da hadin kan Arewa" - Babachir

Jaridar Punch ta rahoto tsohon sakataren gwamnatin yana cewa:

"Mun samu wata kungiyar mutane masu kishin Arewa wadanda suka fara haduwa suna tattauna kan yadda za a shawo kan matsalolin shiyyar.

Kara karanta wannan

ADC: Amaechi ya kada hantar Tinubu kan zaben 2027, ya fadi illar da zai yi masa

"Mun sanya wa wannan kungiya suna NPCP ta Arewa, wacce take dauke da kusan dukkanin manyan 'yan siyasar shiyyar wadanda ba sa tare da gwamnati.
"Manufar hakan ita ce a samar da hadin kai a Arewa. Lallai akwai rarrabuwar kawuna tsakaninmu, kuma mun fahimci hakan zai zama illa garemu a zaben gaba."

"Peter Obi ne ya lashe zaben 2023" -Babachir

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Babachir Lawal ya ce alkaluman da ya tattara sun nuna cewa ba Bola Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa a 2023 ba.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi ne ya samu nasara amma aka canza sakamakon zaben.

Babachir Lawal ya kuma bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin mutum mai girman kai, yana mai cewa shi ne ya masa laifi tun farko amma ya ki karbar laifinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com

iiq_pixel