An Bude wa Gwamnan PDP Kofar Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

An Bude wa Gwamnan PDP Kofar Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa kofarta a bude take ga Gwamna Peter Mbah a duk lokacin da ya shirya sauya sheka daga PDP
  • Tsohon Darakta Janar na VON, Osita Okechukwu ne ya bayyana hakan da yake martani ga ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji
  • Tun farko ministan ya ce duk wanda ke ganin zai shigo APC ya tsaya takarar gwamnan Enugu, to za su gwabza da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Jam'iyyar APC a shirye take ta karbi gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah da mukarrabansa idan har ya amince zai baro PDP ya koma jam'iyya mai mulki.

Tsohon Darakta Janar na Voice Of Nigeria (VON), Osita Okechukwu, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa APC na maraba da gwamna Mbah a ko wane lokaci.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Legas zai bar tafiyar Tinubu ya koma ADC? Ambode ya fayyace gaskiya

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu.
APC ga fara zawafcin Gwamnan Enugu, Peter Mbah Hoto: Peter Mbah
Asali: Twitter

Okechukwu, wanda yana ɗaya daga cikin mambobin APC na farko, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a Enugu a ranar Litinin, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bude wa Gwamna Mbah kofar shiga APC ne a madadin mambobin farko na jam'iyyar APC a Jihar Enugu da Kudu maso Gabas.

Minista na shirin hana gwamna Mbah shiga APC

Sanarwar dai ta mayar da martani ne kan wani jawabi da aka danganta ga Ministan Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji, wanda ya yi magana kan ’yancin Gwamna Mbah na shiga APC.

Tun farko an ji Nnaji yana cewa cewa ba za su daga wa kowa kafa ba, duk wanda zai nemi takarar gwamnan Enugu a inuwar APC zai kara da shi.

“Duk wanda yake son shigowa APC ya nemi takarar gwamnan Jihar Enugu, muna jiransa, za mu fafata da shi ko waye," in ji ministan.

'Jam'iyyar APC ta budewa Gwamna Mbah kofa'

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta yi wa APC illa a mazabar Ganduje a Kano

Da yake martani kan wadannan kalamai, jigon APC ya ce:

“Mu da aka kafa APC da mu, muna so mu bayyana a fili cewa Mai Girma, Dakta Peter Mbah, da tawagarsa, ana maraba da su a APC ta Jihar Enugu.
"Bisa ga al’adar jam’iyyarmu, muna kira ga Gwamna Mbah da tawagarsa kada su ji tsoron kowa.”
Gwamna Peter Mbah.
Kusoshin APC a Enugu sun bukaci Gwamna Mbah ya yi watsi da kalaman Nnaji Hoto: Peter Mbah
Asali: Twitter

Jiga-jigan APC sun soki Ministan Tinubu

Okechukwu ya ce mambobin APC suna mamakin “dalilin da ya sa Nnaji, wanda shi ma ya fito ne daga jam’iyyar PDP, ke kokarin hana Gwamna Mbah duk wata dama ta shiga jam'iyyar."

"Muna bukatar Gwamna Mbah ya yi watsi da maganganun ɗan’uwanmu Cif Nnaji, saboda burinmu shi ne mu karbe gidan gwamnati, mu shiga sahun jihohi 23 don tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a 2027,” in ji shi.

Tsohon Darekta Janar na VON ya shawarci Nnaji da ya fi maida hankali kan ayyukan da ke gabansa a ma’aikatar da Shugaba Tinubu ya nada shi, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Kungiyar gwamnoni ta zabi gwamna 1 da ya fi kowa kokari a 2025

'Yan siyasa sama da 5000 sun koma APC

A wani labarin, kun ji cewa sama da mambobi 5,000 na jam’iyyun LP, PDP da APGA sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Enugu.

Ministan kimiyya da fasaha, Cif Uche Nnaji, tare da shugaban APC na Enugu, Cif Ugochukwu Agballah ne suka karɓi waɗanda suka sauya shekar.

Nnaji ya ce sauya shekar da ake yi zuwa APC alama ce da ke nuna cewa al'ummar Enugu sun fara fahimtar ayyukan da gwamnatin Bola TinubuTinubu ke yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel