ADC Ta Taso APC a gaba, Ta Fallasa Makircin da Ake Shiryawa 'Yan Adawa

ADC Ta Taso APC a gaba, Ta Fallasa Makircin da Ake Shiryawa 'Yan Adawa

  • Jam'iyyar ADC ta nuna rashin gamsuwarta da yadda hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta ke gudanar da ayyukanta
  • ADC ta yi zargin cewa jam'iyyar APC ta mayar da hukumar EFCC karen farautar ta domin yi wa 'yan adawa barazana
  • Jam'iyyar ADC ta nuna cewa hakan ba karamar illa ba ce, yana zubar da kimar hukumar EFCC a idon 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta zargi APC mai mulki da amfani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) a matsayin makami don tsoratar da ‘yan siyasar adawa.

Jam'iyyar ADC ta yi gargadin cewa irin wannan lamari yana lalata amincewar jama’a ga hukumar da kuma raunana yaki da cin hanci a Najeriya.

ADC ta yi zargi kan jam'iyyar APC
ADC ta zargi APC da kokarin murkushe 'yan adawa Hoto: @BolajiADC
Asali: Facebook

Hakan ne kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya a shafin X a ranar Litinin, 11 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: PDP ta amince da bukatun Wike, an gano dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi jam'iyyar ADC ta yi wa APC?

Jam'iyyar ADC ta yi ikirarin cewa a matakan baya-bayan nan na EFCC, ciki har da dawo da ci gaba da tsofaffin shari’o’i da kuma gayyatar mambobin adawa, akwai siyasa a ciki.

"An kafa EFCC ne domin ta kasance mai kare amanar al’ummar Najeriya ba tare da tsoro ba, tana aiwatar da doka daidai ga kowa, aboki ko makiyi, jam’iyya mai mulki ko ta adawa. Yanzu, ba haka abubuwan suke ba."
"Yanzu hukumar tana aiki kamar wani sashen APC, ana amfani da ita don yaƙar masu sukar gwamnati da ‘yan adawa, ta haka tana cimma abin da gwamnati ba za ta iya cimmawa ta hanyar muhawara a bainar jama’a ba."

- Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar ta zargi EFCC da son kai wajen gurfanarwa, tana kawo misalan yadda ake daina bincike kan 'yan siyasar APC yayin da ake ci gaba da farfado da zarge-zargen da ake yi wa ‘yan adawa.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ASUU na barazanar rufe jami'o'in Najeriya saboda yunwa da wasu dalilai

“Tun da wani tsohon gwamna ya koma APC tare da dukkan tsarin siyasar jiharsa, binciken EFCC kan gwamnatinsa ya bace daga idon jama’a. Ba a taba yin tambaya ba. Ba wata takarda da aka fitar. Ba wani sabon bayani."
"A Najeriya ta yau, alamar laifi ko rashin laifi ya dogare ne da jam’iyyar da mutum ke ciki, ba hujja ba."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta nuna yatsa ga jam'iyyar APC
ADC ta yi zarge-zarge kan jam'iyyar APC Hoto: @BolajiADC
Asali: Facebook

ADC ta nuna kuskuren bata ayyukan EFCC

A cewar ADC, irin wannan nuna bambanci yana lalata kimar EFCC da kuma yaki da cin hanci baki daya.

Ta yi gargadin cewa kallon EFCC a matsayin hukumar bi ta kulli kan siyasa yana rage amincewar jama’a kuma yana haifar da rashin amanna kan ayyukanta.

“EFCC ba mallakar APC ba ce. Ta al’ummar Najeriya ce. Da kudaden harajin jama’a ake daukar nauyinta, ba na jam’iyya mai mulki ba."

- Bolaji Abdullahi

Sakaten gwamnatin Buhari ya musanta shiga ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya a zamanin mulkin marigayi, Muhammadu Buhari, Boss Mustapha, ya nesanta kansa da batun komawa jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya yi hangen nesa, ya gano hanyar kwace mulki a hannun APC

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya musanta cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa ADC mai adawa.

Boss Mustapha ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a APC wadda ya ba gudunmawa wajen kafuwarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng