'Rasuwar Buhari ba Za Ta Kawo Cikas ga Tazarcen Tinubu ba a 2027,' Sanata Adeyeye
- Akwai wasu masu sharhi da ke tunanin cewa rasuwar marigayi Muhammadu Buhari za ta iya kawo cikas ga tazarcen Bola Tinubu a 2027
- Sanata Dayo Adeyeye ya bayyana cewa wannan hasashen ko kadan ba daidai ba ne domin Tinubu bai dogara da tasirin Buhari ba
- Ya nuna cewa ko a zaben shekarar 2023, ba tasirin Buhari ba ne ya sanya ya samu nasarar zama shugaban kasa a jam'iyyar APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Tsohon sanata a jihar Osun, Dayo Adeyeye, ya yi magana kan alakar rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tazarcen Bola Ahmed Tinubu.
Dayo Adeyeye ya ce rasuwar marigayi Buhari ba za ta kawo cikas ba ga Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.

Source: Twitter
Adeyeye wanda tsohon karamin ministan ayyuka ne, ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ’yan jarida a ranar Asabar a Legas, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi wannan bayani ne a matsayin martani kan kalaman da wasu ke yi na cewa tasirin Buhari ya taimaka wajen nasarar Tinubu a zaben 2023, kuma rasuwarsa za ta iya kawo cikas ga tazarcensa a 2027.
Rasuwar Buhari ba za ta rage tasirin Tinubu ba
A cewar Adeyeye, tattaunawar da ake yi cewa rasuwar Buhari za ta rage kuri’un Tinubu a Arewa tana kan kuskuren fahimta.
Tsohon ministan, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar South West Agenda for Asiwaju (SWAGA) ya ce Tinubu bai amfani da suna ko farin jinin Buhari a Arewa ba wajen samun nasara a 2023, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Ya bayyana cewa shugaban kasa na ci gaba da samun goyon baya a faɗin ƙasar nan sakamakon ƙoƙarinsa da jajircewarsa.
"Ba daidai ba ne. A gaskiya, Tinubu zai samu ƙarin kuri’u a Arewa da sauran wurare a 2027 fiye da kowane lokaci a tarihin kasar nan."
- Dayo Adeyeye
Dayo Adeyeye ya kuma bayyana cewa ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa cewa bangaren CPC da ke cikin APC ya janye goyon bayansa ga Tinubu.
Ya ce fiye da kashi 90% cikin 100% na mambobin bangaren CPC har yanzu suna goyon bayan shugaban kasan da tazarcensa.

Source: Facebook
Tinubu na da goyon bayan Kudu maso Yamma
Game da jita-jitar cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na shirin yin takara da Tinubu a 2027, Adeyeye ya ce ko da hakan gaskiya ne, ba zai kawo matsala ga tasirin Tinubu ba a yankin Kudu maso Yamma.
Ya ce, ko da yake Gwamna Makinde ya cancanci yin takarar shugaban kasa, wannan buri nasa ba zai zama barazana ga Tinubu ba.
"A’a, ba barazana ba ce kwata-kwata. Babu tasiri. Mutane ba wawaye ba ne. Seyi Makinde mutum ne nagari, gwamna mai kyau kuma mai cancantar yin takarar shugabanci, amma ba zai kwace ko kuri’a ɗaya daga hannun Tinubu a 2027 ba."

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
- Dayo Adeyeye
Tsohon ministan Buhari ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon minista a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya yi bankwana da duniya.
Audu Ogbeh wanda ya taba zama shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya rasu ne a ranar Asabar, 9 ga watan Agustan 2025.
Iyalan tsohon ministan na noma sun bayyana cewa ya yi bankwana da duniya ne cikin lumana bayan ya hidimtawa Najeriya a matakai daban-daban.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

