Fadar Shugaban Ƙasa Ta Dura kan Obasanjo, Ta Yi Masa Gori bayan Shekaru 8 a Mulki
- Fadar shugaban kasa ta ce nasarorin Tinubu cikin shekara biyu sun fi na gwamnatin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007
- Daniel Bwala ya ce PDP a zamanin Obasanjo ta more rangwamen bashi da albarkar man fetur, amma Tinubu ya gaji basussuka
- Ya ƙara da cewa Tinubu ya rage matsalar tsaro sosai, ya ɗauki matakai masu wahala don farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi caccaka kan mulkin jam'iyyar PDP na tsawon shekaru takwas a baya.
Fadar ta bayyana cewa nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta cimma cikin shekara biyu sun zarce aikin jam’iyyar PDP a lokacin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.

Asali: Getty Images
Bwala ya soki mulkin Obasanjo na shekaru 8
Daniel Bwala, mai ba shugaban kasa shawara kan sadarwa, ya bayyana haka a rubutun da ya wallafa a X a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya nuna cewa PDP a lokacin Obasanjo ta more yanayi mai sauƙi, ciki har da rangwamen bashi na waje, ƙarin samar da man fetur, da karɓuwa bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya.
A cewar Bwala, Tinubu ya gaji basussuka masu yawa wanda yake biya, ya kuma fuskanci ƙarancin samar da mai da rashin samun kuɗi daga kasashen duniya.
Ya ƙara da cewa, ba kamar zamanin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007 ba, Tinubu ya hau mulki ne yayin da ake fama da tsanantar matsalar tsaro, wadda ya ce ya rage sosai.
Bwala ya kuma ce, gazawar tattalin arzikin da PDP ta haifar ta sa shugabanni na gaba suna tsoron ɗaukar matakan gyara masu tsauri.

Asali: Twitter
Bwala ya fadi kalubalen da Tinubu ya fuskanta
Bwala ya bayyana cewa Tinubu ya fuskanci kalubalen nan kai tsaye, ya ɗauki matakai masu wuya waɗanda a ganinsa sun saka tattalin arzikin kasa kan hanyar murmurewa.

Kara karanta wannan
Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock
Sanarwar ta ce:
“Abin da Bola Tinubu ya cimma a cikin shekara biyu ya fi abin da PDP ta cimma a shekara takwas daga 1999 zuwa 2007, daga 1999 zuwa 2007 an yafe basussukan waje, Tinubu kuwa sai biya yake yi.
“Daga 1999 zuwa 2007 samar da man fetur ya kasance kamar mu’ujiza idan aka kwatanta da abin da Tinubu ke fama da shi.
“Daga 1999 zuwa 2007 duniya na kallonmu da tausayawa da tallafi bayan dawowar dimokuraɗiyya. Tinubu kuwa sai ya tabbatar da kansa, kuma ya yi hakan da tattalin arziki.
“Daga 1999 zuwa 2007 ’yan Najeriya na haɗe cikin bambance-bambancen su, matsalar tsaro ta yi ƙasa idan aka kwatanta da lokacin da Tinubu ya hau.
Sai dai babu hujjojin da ke tabbatar da cewa a shekaru biyu, Bola Tinubu ya samu nasarorin da suka zarce wanda gwamnatin Olusegun Obasanjo ta samu.
Gwamnatin Obasanjo ta gaji bashi, amma ta yi kokari aka yafe kudin. Legit Hausa ta kuma rahoto cewa gwamnatin Tinubu ta ci bashi akalla sau shida.

Kara karanta wannan
2027: Yadda aka samu shugabanni 2 ko fiye a ADC da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya
Ana zargin Obasanjo bai ci zabe ba
Kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayyya, Cif Olu Falae ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1999, ba Olusegun Obasanjo ba.
Falae, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ya faɗi haka ne domin ƴan Najeriya su san gaskiyar yadda aka dawo mulkin dimokuraɗiyya..
Ya ce tun daga zaɓen 1993 da MKO Abiola ya samu nasara, Najeriya ke fama da matsaloli wajen gudanar da sahihin zaɓe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng