Gwamna Bala Ya Gana da Peter Obi, Ya Miƙa Masa Buƙatar da ka Iya Tarwatsa Haɗakar ADC

Gwamna Bala Ya Gana da Peter Obi, Ya Miƙa Masa Buƙatar da ka Iya Tarwatsa Haɗakar ADC

  • Gwamnan Bauchi ya roƙi tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya dawo jam'iyyar PDP, lamarin da ka iya wargaza haɗakar ƴan adawa
  • Sanata Bala Mohamamed ya yi wannan roko ne yayin da ya karbi bakuncin Oeter Obi da masoyansa a fadar gwamnatin Bauchi yau Juma'a
  • A nasa jawabin, Peter Obi ya ce ya ziyarci Bauchi ne domin tattaunawa da ɗaliban kwalejoji da almajirai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya karɓi baƙuncin ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi.

Peter Obi, ɗaya daga cikin jagororin adawa da suka yi haɗaka a ADC, ya ziyarci Gwamna Bala a gidan gwamnatinsa da ke Bauchi a ranar Juma’a.

Gwamnan Bauchi da Peter Obi.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya karɓi bakuncin Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Gwamna Bala ya bayyana cewa akwai bukatar jam'iyyun adawa su haɗa kansu wuri guda kafin zaɓen 2027, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Najeriya ka iya wargajewa kafin zaɓen 2027': Tsohon minista ya yi hasashe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bala ya nemi jam'iyyu su haɗa kai

Da yake jawabin maraba ga Peter Obi da ƴan Obedient, Gwamnan Bauchi ya ce:

“Ya kamata mu haɗa kanmu don amfanin ‘yan Najeriya. Jam’iyyun adawa dole su haɗu. ADC, PDP da sauran ragowar jam’iyyun siyasa duk ya kamata su haɗa kai.
“Babu ƙiyayya tsakanin mu da gwamnati mai ci, muna fatan za su dawo su yi abin da ya dace, amma kamar yadda na faɗa ku, babu kasafi, babu tsari, tun ranar farko, komai siyasa ce kawai.
“Dole mu yi taka-tsantsan kada mu ci mutuncin jama’armu. Dole mu haɗa kan adawa, mu rage girman kai da son zuciyarmu, domin mu fito da matsaya ɗaya ta ceto ƙasarmu."

Gwamnan Bauchi ya miƙa buƙata ga Peter Obi

Gwamna Bala Mohammed ya ce tsammanin da ‘yan Najeriya ke da shi game da zaɓen 2027 yana da yawa, yana mai rokon Peter Obi da ya dawo jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

An ƙara samun bayanai kan abin da ya sa gwamnonin PDP ke sauya sheƙa zuwa APC

“Don Allah ka dawo gida (PDP), nan ne gidanka na asali, ƙada ka ci gaba da zama a wata jam’iyya da ke cikin rikici.”

A nasa bangaren, Peter Obi ya bayyana cewa ya je Bauchi ne domin tattaunawa da matasa a kwalejojin kiwon lafiya da kuma almajirai.

A cewarsa, a iya tattaunawar da ya yi da waɗanda ya kira shugabannin gobe, ya gamsu da ƙwarewarsu da damar da suke da ita, in ji Vanguard.

Gwamna Bala ya gana da Peter Obi a Bauchi.
Peter Obi ya ziyarci Gwamna Bala domin girmamawa a Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed, @PeterObi
Source: Facebook

Meyasa Peter Obi ya ziyarci Gwamna Bala?

Tsohon gwamnan na jihar Anambara ya yaba wa Gwamna Bala bisa abin da ya kira “kyakkyawan aiki” a fannin ilimi na jihar Bauchi.

Peter Obi ya ce ya ziyarci gwamnan Bauchi ne domin girmamawa da kuma tattauna batutuwan da suka shafe ƙasa domin duba yadda za a haɗu a magance su.

Ƴan Arewa za su zaɓi Peter Obi a 2027?

A wani labarin, kun ji cewa wani jigon APC, Alwan Hassan ya yi ikirarin cewa ƴan Arewa ba za su zaɓi Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasar 2027 ba.

Kara karanta wannan

2027: Bayan hukuncin SDP, ADC ta mika bukata ga El Rufa'i

A cewarsa, ƴan Arewa za su kaucewa shugabancin Peteer Obi ba don komai ba sai don akwai hannunsa wajen shigo da giya a ƙasar nan.

Alwan Hassan ya kuma yi watsi da hadakar 'yan adawa ƙarƙashin jam’iyyar ADC, yana mai cewa ba ta da ƙarfin da za ta ja da APC mai mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262