Lema Ta Yage: Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Yi Murabus daga PDP, Ya ba da Haƙuri
- Tsohon mataimakin gwamna a Najeriya ya jefar da lema bayan sanar da yin murabus daga jam'iyyar da ke adawa a jihar
- Cif Ude Oko-Chukwu wanda ya rike muƙamin a jihar Abia, ya yi murabus daga PDP saboda dalilan kansa, inda ya ce babu yadda ya iya
- Jigon PDP ya gode wa jam’iyyar PDP bisa damar yi masa hidima da kwarewar da ya samu, yana yi musu fatan alheri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia ya tabbatar da yin murabus daga PDP mai adawa a Najeriya.
Cif Ude Oko-Chukwu, ya yi murabus daga jam’iyyar inda ya ce matakin ya zama dole saboda wasu dalilai na karan kansa.

Asali: UGC
Abia: Jigon PDP ya yi murabus daga jam'iyya
Hakan na cikin wata wasika aka aika wa shugaban PDP na mazabar Ndi Elu, Nkporo, karamar hukumar Ohafia ya sanyawa hannu, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasikar, Oko-Chukwu ya bayyana cewa yin murabus dinsa ya faru ne saboda dalilan kansa wanda ya ce ba zai iya kauce hakan ba.
Kodayake tsohon mataimakin gwamnan bai bayyana matakin siyasa na gaba ba, ya ce yanke shawarar barin jam’iyyar PDP abu ne mai wahala a gare shi, amma shi ne mafi alheri a yanzu.
A cikin wasikar, Oko-Chukwu ya tabbatar da cewa:
“Kuna iya lura cewa na yi murabus ne saboda dalilan kaina, duk da cewa shawarar ta yi mani wahalar yankewa, ita ce mafi dacewa a yanzu.
“Ina godiya da damar da jam’iyyar ta bani na yi wa al’umma hidima a matakai daban-daban da kuma kwarewar da na samu a lokacin kasancewata mamba.
“Na gode da fahimtar ku da goyon bayanku a wannan lamari, tare da yi muku fatan alheri a nan gaba.”

Asali: Facebook
Mukaman da Oko-Chukwu ya rike a PDP
Oko-Chukwu, wanda kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Abia ne, ya taba neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Sai dai kuma Oko-Chukwu ya sha kaye a hannun Cif Okey Ahaiwe kafin daga bisani jam'iyyar LP ta lashe zaben, Daily Post ta tabbatar da wannan.
An lura cewa Ama Nwoke Ibe ya karɓa tare da sanya hannu a madadin PDP na mazabar Ndi Elu, Nkporo, a kan wasikar da ya gabatar domin tabbatar da murabus dinsa.
Tsohon sanata a Katsina ya bar APC
Mun ba ku labarin cewa tsohon Sanata daga jihar Katsina kuma babba a APC mai mulkin Najeriya ya yi murabus daga jam'iyyar bayan bauta mata na tsawon shekaru.
Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua, ya fice daga jam’iyyar saboda gazawar gwamnati da rashin adalcin shugabancin jam’iyyar wacce ya ba da gudunmawa sosai wurin kafa ta.
Yar’adua ya bayyana cewa gwamnatin APC ta juya baya ga talakawa tare da aiwatar da manufofin tattalin arziki masu lalata rayuwar 'yan kasa wanda ya jefa al'umma cikin halin kunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng