Ikpeazu, Ude Oko-Chukwu, da wasu Jami'ai sun yi gwajin COVID-19 - Gwamnatin Abia

Ikpeazu, Ude Oko-Chukwu, da wasu Jami'ai sun yi gwajin COVID-19 - Gwamnatin Abia

- Gwamnan Abia ya umarci Kwamishinoninsa su je su yi gwajin cutar COVID-19

- Okezie Ikpeazu ya bada wannan umarni ne bayan mutuwar wani Kwamishina

- An gano cewa Cif Solomon Ogunji ya na dauke da kwayar cutar bayan ya mutu

Mai girma gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu da mataimakinsa, Ude Oko-Chukwu da wasu ‘yan majalisar zartarwar jihar sun gabatar da kansu domin ayi masu gwajin cutar COVID-19.

Punch ta ce shugabannin na jihar Abia sun kai kansu gaban NCDC ayi masu gwajin kwayar cutar COVID-19 bayan an gano cewa wani jami’in jihar da ya mutu ya kamu da wannan cuta.

Kwamishinan harkokin yada labarai na Abia, Cif John Okiyi-Kalu ya bada wannan sanarwa a ranar Litinin, 1 ga watan Yuni, 2020. Hakan na zuwa ne bayan mutuwar Solomon Ogunji.

Rahotanni sun ce an gano Cif Ogunji ya harbu da Coronavirus bayan ya mutu. Ogunji tsohon jami’in jihar ne kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin da ke yaki da annobar COVID-19.

KU KARANTA: An yi kisan kai saboda mangoro a Garin Obingwa a jihar Abia

Ikpeazu, Ude Oko-Chukwu, da wasu Jami'ai sun yi gwajin COVID-19 - Gwamnatin Abia
Gwamnan Jihar Abia Ikpeazu Hoto: Legit
Asali: Depositphotos

“Bayan gwajin da aka yi wa iyalin tsohon ‘dan kwamitin yaki da cutar COVID-19 da kuma majalisar zartarwa, gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu, ya umarci duk ‘yan wannan kwamiti da shugabanni da su ka yi hulda da tsohon kwamishinan su je ayi masu gwajin cutar COVID-19, sannan su killace kansu daga jama’a, har sai lokacin da sakamakon gwajin ya bayyana.”

Jaridar ta ce a ranar Litinin mutane kusan 33 na majalisar zartarwar Abia su ka kai kansu domin ayi masu gwajin cutar. An yi wannan gwaji ne a gidajen kwamishinoni da ke Umuahia.

Kawo yanzu babu wanda wannan cuta ta kashe a fadin jihar. Ko shi kwamishinan da ya rasu kwanakin baya, ba a iya tabbatar da ya na dauke da wannan cuta ba sai bayan ya rasu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng