Shugaban Majalisar Malaman Kano zai Nemi Gwamna, Zai Kara da Abba a 2027

Shugaban Majalisar Malaman Kano zai Nemi Gwamna, Zai Kara da Abba a 2027

  • Sheikh Ibrahim Khalil ya ce zai tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Kano a 2027 karkashin jam’iyyar ADC
  • Malamin ya bayyana cewa ba za a iya kayar da jam’iyyar APC ba sai da hadin kai da sadaukarwa daga ‘yan adawa
  • Sheikh Khalil ya yaba da matakin Atiku Abubakar da Obi Peter Obi na shiga ADC, ya ce hakan abu ne mai kyau a siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban majalisar malaman addini reshen Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2027.

Malamin musuluncin wanda ke daya daga cikin jagororin jam’iyyar ADC a Kano ya yi bayani a kan siyasar jihar da ma Najeriya baki daya.

Shugaban majalisar malaman Kano zai tsaya takara a 2027
Shugaban majalisar malaman Kano zai tsaya takara a 2027. Hoto: Khalil Network
Source: Facebook

Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi a kan siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Abba ya yi magana a fusace bayan 'yan daban Kano sun yi ajalin hadiminsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, yana farin ciki da yadda mutane ke shiga jam’iyyar ADC domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki, musamman ganin yadda abubuwa ke tafiya a kasa.

Sheikh Ibrahim Khalil zai tsaya takara

Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa yana da cikakken shiri da niyya wajen tsayawa takarar Gwamna a Kano a zaben 2027 mai zuwa.

Malamin zai tsaya takara domin karawa da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ake kyautata zaton zai nemi wa'adi na biyu.

A baya dai Sheikh Khalil ya taba tsayawa takarar gwamna a Kano karkashin jam’iyyar ADC amma bai samu nasara ba.

Legit Hausa ta fahimci cewa akwai yiwuwar Ibrahim Little ya nemi tikitin takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar ta ADC.

Ibrahim Little yana cikin jagororin hadaka a Kano kuma ana masa kallon cewa su ne na kusa da Atiku Abubakar a Arewa maso yamma.

ADC za ta iya kayar da APC a 2027?

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC da gwamnoni sun gana da Sheikh Jingir, malaman Izala da Darika

A yayin hirar, Sheikh Khalil ya ce APC ba karamar jam’iyya ba ce, domin tana da karfi da kwarewa wajen fafatawa a zabe.

Ya ce gwamnatin Bola Tinubu tana da shiri na musamman don lashe zaben 2027, don haka jam’iyyun adawa su shirya tsaf idan suna son yin nasara.

Sheikh Khalil ya jaddada cewa babu wata gwamnati da ta yi shirin komawa mulki kamar ta Tinubu a tarihi.

Jam'iyyar ADC ta wallafa a X cewa a shekarar 2022 Sheikh Ibrahim Khalil ya fita daga APC zuwa cikinta.

Hadin kan ‘yan adawa a karkashin ADC

A shekara ta 2025, manyan ‘yan siyasa kamar Peter Obi na LP da Atiku Abubakar na PDP suka shirya hadaka a jam’iyyar ADC.

Wannan mataki ya sanya jam’iyyar ADC ta zama dandali mai karfi da tasiri a siyasar Najeriya, musamman yayin da zaben 2027 ke kara matsowa.

David Mark da wasu shugabannin APC a Abuja
David Mark da wasu shugabannin APC a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A wani mataki na farfado da jam’iyyar ADC, an nada tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya gano babbar matsalar 'yan hadaka, ya ba su.shawara kan 2027

Wannan sauyi ya biyo bayan sauka daga kujerun shugabanci da tsofaffin jagororin jam’iyyar suka yi domin ba wa sababbin jini dama.

An fusata El-Rufa'i kan siyasar 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya fusata kan cewa siyasar shi ta kare.

Tsohon gwamnan ya yi martani da cewa bayan watan Marin na 2027, lokacin da aka kammala zabe za a gane tasirinsa.

'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi game da martanin da Nasir El-Rufa'i ya yi, wasu na goyon bayansa wasu kuma akasin haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng