2027: Tsohon Hadimin Buhari Ya Tono Shirin da Ake Kullawa kan Jonathan

2027: Tsohon Hadimin Buhari Ya Tono Shirin da Ake Kullawa kan Jonathan

  • Tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari, ya yi magana kan wani shiri da ya ce ana kullawa kan Goodluck Ebele Jonathan
  • Bashir Ahmad ya bayyana cewa akwai masu son ganin an kawo tsohon shugaban kasa ya sake neman takara a zaben shekarar 2027
  • Tsohon hadimin na marigayi Buhari ya bayyana cewa ana son yin wannan shirin ne don samun kuri'un 'yan Arewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mai taimaka wa marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya bayyana wani shiri da ake yi kan Goodluck Jonathan.

Bashir Ahmad ya bayyana cewa wasu ’yan siyasa na ƙoƙarin shawo kan tsohon shugaban kasan da ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Bashir Ahmad ya ce akwai shirin da ake yi kan Jonathan
Bashir Ahmad ya ce akwai masu kokarin ganin Jonathan ya yi takara a 2027 Hoto: Bashir Ahmad, Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 4 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Wike ya yi shagube ga Atiku, ya fadi dalilinsa na son kafa hadaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir ya ce ana son yaudarar 'yan Arewa

Tsohon hadimin shugaban kasan ya bayyana matakin a matsayin wata dabara domin samun kuri’un yankin Arewa.

Sai dai, Bashir Ahmad ya ce wannan yunƙurin ya rage kimar Jonathan, yana mai bayyana shi a matsayin dabara ce kawai ta siyasa domin juya tsarin karba-karba bisa tsammanin cewa Jonathan zai yi wa’adin mulki ɗaya ne kawai.

Me tsohon hadimin Buhari ya ce kan Jonathan?

“Daga dukkan alamu, akwai wani yunƙuri cikin sirri daga wasu ‘yan siyasa da ke ƙoƙarin shawo kan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da ya sake tsayawa takara a 2027."
“Sun yi lissafin cewa za a iya tallata shi cikin sauƙi a Arewa da hujjar cewa zai yi wa’adi guda ne kacal.”
“Amma abin damuwa shi ne cewa wannan yunƙurin ba a gina tushensa a kan abin da zai iya yi wa Arewa ko ƙasar baki ɗaya ba, illa dai kawai ya ta’allaka don cika muradun siyasa da tsarin karba-karba na mulki."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ritsa 'yan Boko Haram a daji, an hallaka miyagu

"Arewa ta cancanci fiye da a riƙa amfani da ita a matsayin matakin hawa kan kujerar mulki."

- Bashir Ahmad

Bashir Ahmad ya yi magana kan Jonathan
Bashir Ahmad ya fadi shirin 'yan siyasa kan Jonathan Hotp: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Goodluck Jonathan ya rabu da shugabanci a 2015

Goodluck Jonathan dai ya yi mulki a matsayin shugaban kasa daga 2010 zuwa 2015, inda ya sha kaye a hannun marigayi Muhammadu Buhari a zaben 2015 da tazarar fiye da ƙuri’u miliyan 2.5.

Idan aka tsayar da tsohon shugaban kasan takara kuma ya yi nasara a 2027, kundin tsarin mulki na Najeriya ya ba shi damar yin wa’adin mulki guda ɗaya ne kacal.

Jonathan ya musanta shirin sake yin takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya fito ya yi martani kan batun cewa zai sake yin takara.

Tsohon shugaban kasan ya nesanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya shirya neman babbar kujerar mulki a Najeriya a zaben shekarar 2027.

Goodluck Jonathan ya nuna cewa daga cikin abubuwan da ke gabansa babu batun sake neman kujerar shugabancin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng