"Shawarar da Zan ba Atiku da Ni Ɗansa ne," Ministan Tinubu Ya Ɗauko Tarihi tun daga 1999
- Ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar daga PDP na ci gaba da jawo hankalin manyan jiga-jigai jam'iyyar
- Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tunatar da ƴan Najeriya ɗabi'ar Atiku ta sauya jam'iyya saboda neman mulkin Najeriya
- Wike ya ce idan da shi ɗan Atiku ne da ya zaunar da shi ya nuna masa bai kamata yana yawan sauya sheƙa a shekarunsa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya soki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, bisa yadda yake yawan sauya jam’iyya daga lokaci zuwa lokaci.
Mista Wike ya ce ya kamata Atiku ya san cewa yanzu ya girma, domin magana ake ta shekaru 80 a duniya.

Source: Facebook
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya faɗi haka ne a wata hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin, kamar yadda The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya taɓo tarihin Atiku tun 1999
Ministan ya bayyana cewa tun bayan dawowar Najeriya kan tafarkin dimokuradiyya a 1999, Atiku ya sha sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata.
Ya kara da cewa sauya shekar da ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC a kwanan nan, ba wani sabon abu ba ne dangane da dabi’arsa ta siyasa.
Nyesom Wike ya ce:
"Atiku ya fara da PDP a 1999, daga nan ya koma jam'iyyar AC. Bayan AC ya dawo PDP, daga nan ya koma APC, sai kuma ya dawo PDP, duk domin neman tikitin takarar shugaban kasa."
"Da ace ni ɗansa ne, da na zaunar da shi na ce: 'Baba, me ya sa kake ta yawo daga jam’iyya zuwa jam’iyya alhali ka kai kusan shekara 80 a duniya?'"
Meyasa Atiku ke yawan sauya sheƙa?
Ministan ya ƙara da cewa abin da ke sa Atiku yawan sauya sheƙa shi ne kwaɗayin mulki, yana son zama shugaban ƙasa.
Ya ce Atiku ya fice daga PDP ne saboda ya san ba zai iya samun tikitin takara a karkashin jam’iyyar ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
"Yadda PDP take yanzu, da wuya Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa, don haka ya gaza samun natsuwa, shi ya sa ya koma ya buƙaci ku haɗa kai don kalubalantar Tinubu. Wannan ba daidai ba ne," inji shi.

Source: Twitter
Ministan Tinubu ya caccaki haɗakar ADC
Wike ya kuma yi fatali da hadakar jam’iyyun adawa ta ADC wacce ta lashi takobin kalubalantar shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC a 2027.
A cewarsa, wannan haɗakar ba za ta kai labari ba domin ta tara mutane masu kwaɗayin mulki da son kansu.
Hadimin Wike ya soki sauya shekar Atiku
A wani labarin, kun ji cewa Lere Olayinka, hadimin ministan Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Olayinka ya bayyana cewa ficewar Atiku daga PDP alheri ne ga jam'iyyar, yana mai ƙarawa da cewa ba yanzu ne karonsa na farko da ya canza jam'iyya ba.
Ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar mutum ne mai yawan sauya jam’iyya, wanda ya mayar da kansa tamkar makami da ake amfani da shi wajen rusa PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

