Yar'adua: Sanatan APC Ya Tsage Gaskiya kan Ficewa daga Jam'iyyar

Yar'adua: Sanatan APC Ya Tsage Gaskiya kan Ficewa daga Jam'iyyar

  • Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki
  • Ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a ciki domin har yanzu shi cikakken mamba ne a jam'iyyar APC
  • Sanatan mai wakiltar Katsina ta Tsakiya ya bayyana cewa ba kowane mai suna Yar'adua ba ne yake da alakar siyasa da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Abdulaziz Musa Yar’Adua, sanata mai wakiltar yankin Katsina ta Tsakiya, ya yi magana kan jita-jitar ficewa daga jam'iyyar APC.

Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken ɗan jam’iyyar APC ne.

Abdulaziz Yar'adua ya musanta ficewa daga APC
Sanata Abdulaziz Yar'adua ya ce har yanzu yana cikin APC Hoto: @AbdulazizYaradua
Asali: Twitter

Sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 3 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulaziz Yar'adua ya musanta ficewa daga APC

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, tsoho 'dan majalisar tarayya ya sauya sheka

Abdulaziz Yar'adua ya bayyana rahotannin da ke cewa ya fice daga jam’iyyar mai mulki a matsayin “jita-jita marasa tushe kuma masu ɗauke da mugun nufi.”

"Ina so na jaddada cikakken goyon bayana da kuma ɗorewar biyayyata ga jam’iyyar APC."
"Ina kira ga kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da duk wani taken jita-jita da ke nuna cewa na fice daga jam’iyyar."

- Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua

Yar’Adua ya ce ba dukkan masu ɗauke da sunan Yar’Adua ne ke da alaƙar siyasa da shi ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da hakan.

Ɗan majalisar ya zargi wasu kafafen yaɗa labarai da ƙoƙarin kawo ruɗani ta hanyar alaƙanta wasu mutane da ba su da alaƙa da shi ga sunansa.

“Abu ne mai matuƙar muhimmanci a fayyace cewa ba kowane mai suna Yar’Adua ke da alaƙar siyasa da ni ba."
"A matsayina na shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojoji da kuma shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, ina ci gaba da aiki tare da shugabancin majalisar domin inganta dokoki da za su tallafa wa ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu."

Kara karanta wannan

Katsina: Bayan bautawa APC na shekaru, Sanata Yar'Adua ya bar jam'iyyar, ya shiga ADC

- Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua

Abdulaziz Yar'adua ya ce yana nan daram a APC
Abdulzaziz Yar'adua ya musanta ficewa daga APC Hoto: @AbdulazizYaradua
Asali: Twitter

Sanata Yar'adua ya yabi gwamnatin Tinubu

Sanatan ya yaba da yadda gwamnatin Tinubu ke ƙara kuɗi zuwa ga jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma saka hannun jari a sassa masu muhimmanci kamar noma, gine-ginen tituna, da ɗaukar ma’aikatan tsaro.

"A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun shaida ƙoƙari daga shugaban ƙasa wajen ƙara yawan kuɗin shiga ga jihohi da ƙananan hukumomi, saka hannun jari a muhimman ababen more rayuwa, da kuma ƙarfafa tsarin tsaro,” in ji shi.
"A matsayarmu na shugabannin siyasa, dole ne mu marawa shugaban ƙasa baya domin tabbatar da cewa waɗannan gyare-gyaren da ya ke yi sun amfanar da talakan Najeriya."

- Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua

Sanata Yar'adua ya fice daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata a jihar Katsina, Abubakar Sadiq Yar'adua ya fice daga jam'iyyar APC.

Tsohon sanatan ya zargi tsohuwar jam'iyyarsa ta APC ta rashin shugabanci na gari da lalata tattalin arzikin kasa.

Ya nuna cewa jam'iyyar APC tana fifita wasu 'yan tsiraru fiye da jin dadin dumbin talakawan da take jagoranta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel