ADC: El Rufai da Manyan Ƴan Siyasar Kaduna da Suka Fice daga PDP, APC, Suka Shiga Haɗaka
Kaduna - Tun bayan bayyana ADC a matsayin dandalin hadakar ’yan adawa, jam’iyyar ta fara jawo hankalin manyan ’yan siyasa a Kaduna da sauran jihohin Najeriya.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit Hausa ta rahoto cewa manyan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da jam’iyya mai mulki APC, na ci gaba da komawa ADC musamman a Arewa maso Yamma.

Source: Twitter
Sauyin sheka zuwa jam'iyyar ADC a Kaduna
The Nation ta rahoto cewa haɗakar ADC ya ɗauko ɗaruruwan ƴan siyasa daga APC, PDP, da sauran jam'iyyu a jihar Kaduna, lamarin da wasu ke ganin zaɓen 2027 zai yi zafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da wasu ke ganin mutanen da suka shiga hadakar na da karfi kuma barazana ce ga APC, wasu kuwa na ganin bai da wani tasiri kuma ba za su iya taɓuka komai ba.

Kara karanta wannan
Bayan ya baro PDP, Sanata Melaye ya kawo hanyar da ADC za ta buga Tinubu da ƙasa a 2027
A Kaduna, babban jigon da sauya sheƙarsa ta ɗauki hankali shi ne tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya taba rike mukami a APC kuma da shi aka kafa jam'iyyar.
Manyan jagororin haɗakar ADC a Najeriya
El Rufai'i ya shiga tawagar haɗaka da ta ƙunshi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, Peter Obi da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola na cikin jagororin wannan haɗaka.
Manyan jiga-jigai 4 da suka shiga ADC a Kaduna
A wannan rahoton, Legit.ng ta jero manyan ’yan siyasa hudu daga jihar Kaduna da suka fita daga jam’iyyunsu domin shiga sabuwar hadakar ADC.
1. Nasir Ahmad El-Rufai
A farkon watan Yuli, 2025 aka yi taron hadakar ƴan adawar Najeriya a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, inda aka bayyana ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita.
El-Rufai da wasu jiga-jigan ’yan siyasa daga sassa daban-daban na kasa sun halarci taron. Sai dai har yanzu El-Rufai bai kammala shiga jam'iyyar ADC ba.

Kara karanta wannan
Gwamna ya shirya zama na farko da zai shiga jam'iyyar haɗaka, ADC? An samu bayanai

Source: Twitter
Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa an ba shi lokaci domin ya kammala wasu al’amura da suka rage masa a tsohuwar jam’iyyarsa, wato SDP.
Tun farko El-Rufai ya sanar a shafinsa na Facebook cewa ya koma jam'iyyar SDP bayan ficewa daga APC, amma dai yana cikin haɗakar adawa kafin su yanke jam'iyyar da za su shiga.
2. John Ayuba
John Ayuba, wanda ya kasance dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kaduna a karkashin PDP a zaben 2023, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Channels TV ta tattaro cewa Ayuba ya taɓa rike muƙamin Kwamishinan Harkokin Kudi a jihar Kaduna.

Source: Twitter
Ya tabbatar da sauyin shekarsa ta hanyar wasikar murabus da ya rubuta wa shugaban PDP na Unguwan Gaiya da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Kaduna ranar Litinin, 28 ga watan Yuli, 2025.
Ya bayyana cewa rashin tsari da kuma gazawar shugabanci a matakin kasa ne ya sa ya bar jam’iyyar, yana mai zargin jagororin PDP na kasa da lalata makomar jam’iyyar.
3. Aliyu Bello
Aliyu Bello, wanda shi ne sakataren kudi na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, ya yi murabus daga matsayinsa tare da fita daga jam’iyyar baki ɗaya.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ya koma jam’iyyar ADC domin shirin tunkarar babban zaben 2027.
Bello, wanda sananne ne a matsayin tsohon jigo a PDP kuma na kusa da Atiku Abubakar, ya aike da wasikun murabus guda biyu daban-daban, dukkansu rana guda, Laraba, 16 ga Yuli, 2025.

Source: Facebook
Ya tura wasiƙun zuwa shugaban PDP na jihar Kaduna da kuma shugaban jam’iyyar na mazabarsa ta Tudun Nupawa.
A cikin wasikarsa zuwa ga shugaban jam’iyyar jihar, Bello ya rubuta cewa:
“Na rubuta wannan wasika ne domin sanar da ku hukuncin da na yanke na yin murabus daga matsayin sakataren kudi na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, wanda zai fara aiki daga ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2025.”
Manufar kafa haɗakar adawa ta ADC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa sun kafa haɗaka ne domin cika burunsu na samun mulki.
Atiku ya ce an kafa hadakar ne da nufin ceto dimokuraɗiyyar Najeriya daga danniya da take-taken maguɗin zaɓe da jam’iyyar APC ke yi.
Jagoran adawar ya nuna damuwa kan yadda APC ta naɗa tsohon kwamishinan zaɓen a matsayin shugabanta na ƙasa, yana mai zargin cewa akwai wani shiri a ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

