Jibrin Kofa: NNPP Ta Yi Magana bayan Dan Kwankwasiyya Ya Gana da Tinubu

Jibrin Kofa: NNPP Ta Yi Magana bayan Dan Kwankwasiyya Ya Gana da Tinubu

  • Jam’iyyar NNPP ta ce ba ta da wani shiri na hukunta Abdulmumin Jibrin kan ganawarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Sakataren yaɗa labaran NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya ce Jibrin Kofa bai aikata wani abu da ya sabawa jam’iyya ba
  • A wata hira da ya yi, Jibrin Kofa ya bayyana cewa komai zai iya yiwuwa a siyasance, amma bai bayyana ko zai koma APC ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar NNPP ta ce ba za ta ɗauki wani matakin ladabtarwa ko hukunci ba kan ɗan majalisar tarayyar Kiru/Bebeji na jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa.

NNPP ta yi magana ne bayan Jibrin Kofa ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Villa.

Kara karanta wannan

ADC: 'Yadda gwamnoni da hadimai ke cika kunnen Tinubu da karya da gaskiya'

Dan majalisar NNPP tare da shugaba Bola Tinubu
Dan majalisar NNPP tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Abdulmumini Jibrin Kofa
Source: Twitter

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi da jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin hirar, Ladipo Johnson ya ce ganawar Jibrin Kofa da shugaban ƙasa ba ta sabawa manufofin jam’iyyar ba.

Tinubu: Jibrin bai yi laifi ba inji NNPP

Johnson ya bayyana cewa babu wani abu da Jibrin ya aikata da za a iya cewa ya sabawa jam’iyyar, domin an san da ganawar tun kafin ta faru.

Ya ce:

"A’a, babu wani shiri na hukunta shi. Idan ka tattauna da mutane daga jam’iyya mai mulki ko da shugaban ƙasa ne kuma jam’iyyar ka ta san da hakan, ba wanda zai zarge ka da cin amanar jam’iyya.
"Don haka, har yanzu ba lokacin da ya dace ne a fara maganar hukunci ba. Mun sha nanata cewa NNPP jam’iyya ce mai bin tsarin dimokuraɗiyya.”

NNPP ta ce tana bin dimokuradiyya

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yi fatali da tsarin jam'iyya mai mulki, ya yi barazanar sauya sheƙa

Johnson ya ƙara da cewa jam’iyyar NNPP tana da fahimta kan cewa mutane na iya sauya matsayi a siyasa, amma abin da ke da muhimmanci shi ne ci gaban jam’iyyar da ƙasa gabaɗaya.

A cewar Johnson:

“Mun sha bayyana wa a baya cewa jam’iyyarmu na bin tsarin dimokuraɗiyya ne."
Rabiu Kwankwaso tare da Bola Tinubu a 2023
Rabiu Kwankwaso tare da Bola Tinubu a 2023. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Rade-radin sauya sheka zuwa APC

Ganawar da aka yi tsakanin kofa da shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba ta haifar da rade-radin cewa akwai yiwuwar Jibrin zai fice daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Jibrin, wanda aka san kusancinsa da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya amsa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa cewa komai zai iya yiwuwa a siyasa.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana da shirin sauya sheka zuwa APC, sai ya amsa da cewa:

“Ban yanzu ne lokacin irin wannar tattaunawa ba. Amma komai a bude yake,"

Kwankwaso ya ziyarci Aso Rock Villa

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci fadar shugaban kasa a watan Yuli da ya wuce.

Kara karanta wannan

Adamu Garba ya tunawa ƴan Najeriya abin da suka manta tun Buhari na raye a 2015

Sanata Rabiu Kwankwaso ya halarci wani taro ne na bunkasa tattali da aka yi a Abuja tare da hadin gwiwar fadar shugaban kasa.

Ziyarar Kwankwaso ta jawo magana sosai a fagen siyasar Najeriya, musamman saboda rade radin da ake na cewa zai koma APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel