'PDP Ta Shiga Wani Hali,' Sanata Dino Melaye Ya Yi Bankwana da Jam'iyyar Adawa

'PDP Ta Shiga Wani Hali,' Sanata Dino Melaye Ya Yi Bankwana da Jam'iyyar Adawa

  • Sanata Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance, yana mai cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikinta ba
  • A cikin wasikar da ya aikawa shugaban PDP na mazabarsa, Melaye ya zargi wasu manyan jam’iyyar da jawo lalacewar tsari da tasirinta
  • Ficewar Melaye ta nakasa PDP a Kogi, yayin da ake hasashen za ta koma jam’iyyar APC ko kuma ya shiga ADC domin takara a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi – A wani mataki da zai iya girgizar siyasar Najeriya, Sanata Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP a hukumance.

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kogi, karkashin PDP ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata, 4 ga Yulin 2025.

Kara karanta wannan

ADC ta samu ƙaruwa, babban jigon PDP a Kaduna ya sauya sheƙa

Sanata Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar adawa ta PDP
Sanata Dino Melaye ya ce PDP ta rasa karfin da za ta ceto Najeriya. Hoto: @_dinomelaye
Source: Facebook

Dino Melaye ya fice daga jam'iyyar PDP

Legit Hausa ta samu kwafin takardar murabus din tsohon sanatan a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a ranar 31 ga Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dino Melaye ya aika da wasikar murabus din ne zuwa ga shugaban jam'iyyar PDP na Ward 1 da ke Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu, jihar Kogi.

Fitaccen dan siyasar ya ce yanzu jam'iyyar PDP ta rasa “ƙarfi da damar” da za ta iya ceto ƴan Najeriya daga halin da suke ciki.

Ya kuma zargi wasu kusoshin jam'iyyar da zama silar da ya sa PDP ta lalace yanzu, har ma ta rasa kimar da zai iya ci gaba da zama a cikinta.

"Ba zan iya c gaba da zama ba" - Dino Melaye

A cikin wasikar, Sanata Dino Melaye ya ce:

"Bayan na yi nazari mai zurfi kan halin da jam'iyyar take ciki a yanzu, na yanke shawarar cewa ba zan iya ci gaba da shiga cikin ayyukanta ba, ko kuma in ba da goyon baya ga tsare-tsarenta.

Kara karanta wannan

'Za mu shiga Aso Rock': Atiku ya fadi babban shirin ADC na karbar mulki a 2027

"Saboda haka, ina fatan za a ɗauki wannan wasikar a matsayin janyewa ta a hukumance daga jam'iyyar da dukkan ayyukanta a dukkan matakai."

Ficewar Dino Melaye daga PDP ya biyo bayan rikice-rikice da ya samu da jam'iyyar a baya, inda har aka dakatar da shi a 2024 kan zargin yiwa jam'iyya zagon kasa.

Ana hasashen jam'iyyar da Melaye zai koma

Murabus din tsohon sanatan dai ta kara shiga cikin tarihin siyasarsa na sauya sheka a tsakanin jam'iyyu, inda a 2018 ya fice daga APC zuwa PDP, inji wani rahoto na The Nation.

Har yanzu dai ba a san jam'iyyar da Sanata Dino Melaye zai koma ba bayan barin PDP, amma ana rade-radin cewa zai iya shiga jam'iyyar hadaka ta ADC don yin takara a 2027.

Sai dai kuma, wasu na ganin cewa zai iya komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC, domin hada hannu da Shugaba Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

A yanzu dai, sauya shekar Dino Melaye za ta iya raunana karfin PDP a jihar Kogi, kasancewar ya yi takarar gwamna a zaben da ya gabata a karkashin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta haƙura da Kano, ta sauya wuri da ranar gudanar da babban taron ƙasa

Karanta wasikar a kasa:

Surukar Sanata Dino Melaye ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, surukar tsohon dan takarar gwamna a jihar Kogi karkashin jam'iyyar PDP, Dino Melaye ta rasu.

Sanata Melaye ya tabbatar da mutuwar matar kaninsa Timothy Melaye a ranar Alhamis 5 ga watan Disambar 2024.

Marigayiyar mai suna Damilola Melaye ta rasu ne a ranar Laraba 4 ga watan Disambar 2024 a Lagos bayan fama da rashin lafiya

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com