ADC Ta Yi Bayani kan Rashin Sauya Sheƙar El Rufa'i da Obi har Yanzu
- Jam’iyyar ADC ta tabbatar da cewa Peter Obi da Nasir El-Rufa’i ba za su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ba tukuna
- Wannan na zuwa ne bayan gargaɗin shugaban rikon kwarya na ADC, David Mark na cewa na za lamunci raba ƙafa na
- A ƙarin haske da ta yi kan batun, ADC ta ce akwai waɗanda aka amince su ci gaba da zama a jam'iyyunsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jam'iyyar ADC ta fayyace dalilin da ya sa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaben 2023, Peter Obi, bai dawo haɗakar adawa ba tukuna.
Kazalika, jam’iyyar ta bayyana cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i da Obi, ba za su sauya sheƙa daga jam’iyyunsu na yanzu ba, yayin da ake shirin 2027.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Bolaji Abdullahi, sakataren yaɗa labaran ADC na ƙasa ne ya tabbatar da hakan a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba.
Bayanin na zuwa ne bayan ADC ta gargaɗi ƴaƴanta a kan mayar da hankali kacokan a kanta ba raba ƙafa ba.
Gargaɗin jam'iADC ga ƴaƴanta
Daily Post ta ruwaito shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, ya yi gargaɗin ewa ba za a lamunci rashin da’a ko sabawa tsarin jam’iyya ba.
A cewarsa:
“Ba za mu amince da cin amanar jam’iyya ko rashin da’a ba. Kana cikin ADC ko kuma babu kai. Babu zama a raba kafa ba. Duk wanda ba ya tare da mu, ba za mu tafi da shi ba."
“Za mu sake fasalin tsarin shugabanci daga tushe har matakin ƙasa, domin ya dace da sababbin ƙalubalen da ake fuskanta. Za mu buɗe ƙofofi ga matasa.”

Kara karanta wannan
Ana shirya yadda za a shigo Arewa a kayar da Atiku, Kwankwaso da wasu jiga jigai a 2027
ADC na neman Obi da El-Rufa’i gabanin 2027
Ana ganin jam’iyyar ADC, wadda aka amince da ita a matsayin dandalin haɗakar ‘yan adawa na ƙoƙarin janyo Obi da wasu manyan ‘yan siyasa su dawo cikinta a hukumance.
Sai dai masu mara wa Obi baya sun yi watsi da gargaɗin David Mark, inda suka ce shugaban nasu ya riga ya bayyana matsayinsa ga jagororin haɗin guiwar tun da farko.

Source: Twitter
Shugaban ƙungiyar Obidient, Dr Yunusa Tanko, ya ce ba za su bari a matsa wa Obi lamba har ya yanke hukunci da gaggawa ba.
A cewarsa:
“Kafin ma a fara batun wannan haɗin guiwa, shugabanmu ya bayyana matsayinsa tun farko cewa har yanzu yana tare da jam’iyyar LP."
“Obi ya bayyana wannan tun lokacin da aka fara kafa haɗin gwiwar. Don haka, ba mu ga wani sabon abu ba, domin tun farko mun bayyana matsayarmu.”
Da aka tuntubi Bolaji Abdullahi domin ya tabbatar da wannan bayani, ya ce jam’iyyar ta bayar da dama ta musamman ga Peter Obi da El-Rufa’i su ci gaba da kasancewa a jam’iyyunsu.
Jigon PDP ya komajam'iyyar ADC
A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamna kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Kano, Ibrahim Ali Amin Little ya sanar da sauya sheƙa.
Wannan mataki na Little ya fito ne ta cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Tudun Wada, tare da bayyana koma wa ADC.
Ali Ali Amin Little yace rikice-rikicen cikin gida da rashin mutunta dimokuraɗiyya da ƙa’idoji ne su ka janyo ya fice daga PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

