ADC Ta Raba Gardama kan Batun Kafa Hadaka don Cika Burin Atiku Abubakar

ADC Ta Raba Gardama kan Batun Kafa Hadaka don Cika Burin Atiku Abubakar

  • Jam'iyyar hadaka watau ADC ta fito ta yi magana kan wasu maganganu da ake jifanta da su dangane da Atiku Abubakar
  • Sakataren yada labaran ADC na kasa ya bayyana cewa ba a kafa jam'iyyar ba don cika burin Atiku na zama shugaban kasa ba
  • Mallam Bolaji Abdullahi ya nuna cewa a halin yanzu, jam'iyyar ba ta da wani dan takarar da take goyon baya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta fito ta yi magana kan batun cewa an kafa hadaka ne domin cika burin Atiku Abubakar na yin takarar shugaban kaaa.

Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa hadakar ba domin burin takarar shugabancin ƙasa na Atiku Abubakar ba ne a zaben 2027.

ADC ta yi magana kan Atiku Abubakar
ADC ta ce ba ta da dan takarar da take goyon baya Hoto: @atiku
Source: Twitter

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na Channels Tv a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

ADC: 'Yadda gwamnoni da hadimai ke cika kunnen Tinubu da karya da gaskiya'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta yi karin haske kan Atiku Abubakar

Bolaji Abdullahi ya ce maganar cewa ADC wata kafa ce da aka gina domin cika burin Atiku, ƙage ne wanda waɗanda ba sa son ganin hadakar ta samu nasara suka ƙulla.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta da wani ɗan takara da take marawa baya.

"ADC ba jam’iyyar da aka gina wa Atiku ba ce. Wannan ba hadakar Atiku ba ce kwata-kwata."

- Mallam Bolaji Abdullahi

Mai magana da yawun jam’iyyar ADC ya bayyana cewa labarin danganta hadakar da Atiku an ƙirƙire shi ne tun kafin a fara taron hadakar.

Ya ƙara da cewa:

"Ni da nake da shekara 56, wa ya ce ba zan iya neman shugabancin ƙasa ba?"

Me jam'iyyar ADC ta ce kan Peter Obi?

Game da dangantakar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da ADC, Bolaji Abdullahi ya ce Obi yana da cikakken kishin hadakar.

Kara karanta wannan

'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027

ADC ta yi maganganu kan Atiku Abubakar
ADC ta ce Peter Obi na cikin hadaka Hoto: @bolajiADC
Source: Facebook

Ko da yake har yanzu bai zama ɗan jam’iyyar ADC ba, Bolaji Abdullahi ya jaddada cewa Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, an ba su izini daga ADC su kammala harkokinsu na zaɓe a jam’iyyun LP da SDP.

Ya kuma ce Peter Obi ba zai koma PDP ba, wacce ya bayyana a matsayin jam'iyyar da ke neman kowane ɗan siyasa da zai iya taimaka mata ta dawo kan hanya.

Yayin da yake amsa tambayar dalilin da ya sa ’yan Najeriya za su yarda da jam’iyyarsu, Bolaji Abdullahi ya ce APC ta yi alkawarin sauyi amma ta gaza, don haka lokaci ya yi da Najeriya za ta gwada wani sabon abu.

Atiku ya fadi manufar kafa hadaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan hadakar 'yan adawa.

Atiku ya bayyana cewa an kafa hadaka ne ba don ganin cewa an raba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mulki ba.

Ya nuna cewa manufar kafa hadakar ita ce don ganin an ceto Najeriya daga cikin halin da ta tsinci kanta a ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng