'Ban da Peter Obi': An Yi Wa Malami Wahayi game da Mutum 3 da Za Su Fatata a 2027
- Fasto Elijah Ayodele ya yi magana kan waɗanda za su tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ke tafe
- Ayodele ya ce takarar shugaban kasa ta 2027 za ta kasance tsakanin Bola Tinubu da wasu mutane biyu da aka nuna masa
- Ya gargadi Peter Obi ka da ya tsaya takara, domin yin hakan zai sauƙaƙa wa Tinubu samun wa'adi na biyu a zaben shugaban kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fasto Elijah Ayodele na 'INRI Evangelical Spiritual Church' ya ja kunnen tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.
Fasto Ayodele ya bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2027 zai kasance ne tsakanin Bola Tinubu da wasu mutane biyu.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani bidiyo da malamin ya yada a shafinsa na Facebook a farkon wannan mako a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya ce an yi masa wahayi cewa mutane ukun da za su fafata, amma ya ƙi bayyana sunayen biyun, ya ce ba su ne Obi da Amaechi ba.
Shirin da yan adawa ke yi domin 2027
A baya dai an bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ƙaddamar da wata ƙungiyar haɗin gwiwa da ta haɗa da Rotimi Amaechi da Obi.
Wannan ƙungiya ta ɗauki jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasar ta, inda David Mark da Rauf Aregbesola suka zama shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar.
Tun daga lokacin, ADC ta zama babbar jam’iyyar adawa, tana sukar APC tare da shiryawa tsaf don fuskantar ta a zaɓen 2027.
Atiku, Obi da Amaechi duk sun nuna sha’awar tikitin shugaban ƙasa na ADC, inda Obi da Amaechi suka ce za su yi wa’adi ɗaya ne kawai.

Source: Facebook
'Matsalar da Obi zai kawo a 2027' - Fasto
Fasto Ayodele ya bayyana cewa idan aka sa Peter Obi ya tsaya takara a 2027, hakan zai sauƙaƙa wa Bola Tinubu samun wa'adi na biyu.
Ya ce mutanen biyu da aka nuna masa su ne kaɗai za su iya wahalar da Tinubu, amma Obi ba zai iya kawo cikas ba.
Ya yi gargadin cewa Obi bai dace da shugabanci a 2027 ba, ya kuma ce kada ya ci gaba da ba da tallafi a Arewa, cewar rahoton Legit.ng.
Malamin ya ce Arewa ba su son Obi, suna so Musulmi ne ya ci gaba da mulki, saboda haka Obi ya daina kashe kuɗi a yankin.
Fasto ya fadi hanyar kayar da Tinubu
Mun ba ku labarin cewa fitaccen Fasto Elijah Ayodele ya bayyana dabarun da ya kamata ƴan adawa su yi idan suna son kayar da jam'iyya mai mulki a babban zaɓe na gaba.
Malamin cocin ya faɗi dabarun ne a lokacin da ƴan siyasa suka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya.
Ayodele ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi duk mai yiwuwa domin ya ci gaba da mulkin ƙasar nan har tsawon shekaru takwas ba tare da wata matsala ba.
Asali: Legit.ng

