"Ba don Tinubu ba ne": Atiku Ya Fadi Manufar Kafa Hadakar 'Yan Adawa a ADC
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tabo batun manufar kafa hadakar 'yan adawa karkashin ADC
- Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba an kafa hadakar ba ne don cika muradun kashin kai na jagororinta ba
- Tsohon dan takarar shugaban kasan ya nuna manufar kafa hadaka ita ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a karkashin mulkin APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa karkashin ADC ba ta ta’allaka ba ne kawai a kansa, Peter Obi, Rotimi Amaechi, ko Nasir El-Rufai ba.
Atiku Abubakar ya ce an kafa hadakar ne da nufin ceto dimokuraɗiyyar Najeriya daga danniya da take-taken maguɗin zaɓe da jam’iyyar APC ke yi.

Source: Twitter
Atiku ya bayyana haka ne ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mazi Paul Ibe, cikin wata hira ta musamman da jaridar Vanguard jiya a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace manufa hadakar ADC ke son cimmawa?
Ya jaddada cewa babban burin haɗakar ita ce kare mutuncin dimokuraɗiyyar Najeriya, wadda ya ce take fuskantar barazana daga gwamnatin jam’iyyar APC.
"Wannan ba wani aikin adawa da Tinubu ba ne, wannan wani yunƙuri ne na goyon bayan Najeriya. Dole ne 'yan Najeriya su amfana daga wannan ƙoƙari."
- Paul Ibe
Atiku ya zargi APC mai mulki da fara shiri domin yin maguɗin zaɓe a shekarar 2027, inda ya nuna damuwa kan nadin tsohon jami’in hukumar INEC, wanda ya taɓa shugabantar sashen fasahar sadarwa (IT), a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
"Nadin tsohon kwamishinan zaɓe na INEC a matsayin shugaban APC na kasa abin damuwa ne matuƙa. Ba wani tsohon jami’i ne kawai ba; wannan mutum ne da ya rike matsayi mai muhimmanci, irin na shugaban sashen fasahar sadarwa na INEC."
"Wannan mataki na nuna cewa jam’iyyar mai mulki ba ta da niyyar samun nasara ta hanyar bin ƙa’ida ko aikin da ta yi a wa’adin ta na farko. Maimakon haka, suna shimfiɗa tubalin yin maguɗin zaɓe a nan gaba.
- Paul Ibe

Source: Facebook
Atiku ya ba 'yan tafiyar hadaka shawara
Atiku ya jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin jam’iyyun adawa da shugabanninsu.
"Duk wata rarrabuwar kawuna a tsakaninmu za ta amfani waɗanda ke son ƙwace mulki ta kowane hali, da waɗanda ke son ci gaba da rike madafun iko, za su yi amfani da kowane gibi a cikin tsakaninmu."
"Hadin kai shi ne ƙarfimu. Idan muka tsaya tsayin daka tare, zai yi wahala a zuga mu ko a raba kanmu."
"Wannan tafiyar ba don Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, ko wasu ba ne. Tafiya ce game da makomar Najeriya da walwalar ’yan ƙasa. Game ne da ba wa ’yan Najeriya damar farfaɗowa da gina ƙasarsu."
"Wannan shi ne asalin aikinmu, kuma dole mu riƙa tuna wa kanmu da hakan a kullum yayin da muke aiki tare."
- Paul Ibe
Atiku ya bugi kirji game da zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya bugi kirji kan zaben shekarar 2027.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ta 'yan hadaka za ta shiga fadar Aso Rock bayan ta karbi mulki.
Ya nuna kwarin gwiwar cewa shirin da ADC zai sanya ta samu nasarar hambarar da gwamnatin jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


