'Za Mu Shiga Aso Rock': Atiku Ya Fadi Babban Shirin ADC na Karbar Mulki a 2027
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar ADC za ta lashe zaben shugaban kasa a 2027 tare da karɓar mulki daga hannun APC
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ADC na da tsayayyen tsari da akida don ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki
- Tsofaffin jiga-jigan APC, PDP da kuma SDP sun koma ADC, yayin da aka nada sababbin shugabannin jam'iyyar a jihar Ekiti
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bugi kirji da cewa jam’iyyar ADC za ta shiga fadar Aso Rock Villa a 2027.
Atiku ya ce yana da yakinin cewa shirin da jam'iyyar hadakar 'yan adawar ta yi zai ba ta nasarar karbar mulki daga hannun APC a zabe mai zuwa.

Source: Getty Images
Atiku ya gana da tsofaffin 'yan APC, PDP
A rahoton da jaridar Leadership ta fitar, an ji Atiku Abubakar, ya koka kan yadda jam’iyyun siyasa ke fama da rashin akida a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP ya ce ADC ta zo da wani tsari da manufofi don magance matsalolin tattalin arziki da sauran kalubalen ƙasa.
Ya yi wannan jawabi ne a garin Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin ƙaddamar da shugabannin jam’iyyar ADC na jihar, wanda ya samu halartar tsofaffin kusoshin APC, PDP da SDP.
Atiku, wanda Farfesa Bayode Fakunle ya wakilta, ya ce siyasar Najeriya ta canza, kuma yanzu akwai jam’iyyu da dama da ba su da akida.
A cewarsa:
“An ƙaddamar da jam’iyyar ADC ne kusan makonni uku da suka gabata, amma cikin makonni biyu kacal, ta zama jam’iyya mafi ƙarfi a ƙasar nan.
'ADC za ta karbi mulki a 2027' - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tun bayan kaddamar da ADC ne sauran jam'iyyu suka rikici, yana mai cewa:
"Wannan ne ya jefa sauran jam’iyyu cikin firgici, saboda sun fahimci cewa ADC ta dauko hanyar karbar mulki a 2027."
Jaridar Daily Post ta rahoto Atiku ya kara da cewa:
“ADC jam’iyya ce mai tsari da akida, wacce ke cike da mutane masu kishin Najeriya da niyyar ceto ta daga halin da take ciki.
"Samar mata da akida da cika ta da mutane masu kishi, ya sa ADC ta zama jam'iyyar adawa mafi girma a fagen shirin lashe kowane irin zabe.
“ADC jam’iyya ce ta kowa da kowa, kuma za ta sauya tsarin siyasar Najeriya. Da yardar Ubangiji, ADC za ta karɓi mulki a 2027.”

Source: Facebook
Tsofafin ‘yan PDP, SDP da APC sun shiga ADC
Cikin wadanda suka shiga jam'iyyar ADC akwai tsohon mataimakin gwamnan Ekiti, Farfesa Kolapo Olusola Eleka, wanda yanzu shi ne jagoran jiga-jigan ADC a jihar.
Sauran sun hada da tsohon sakataren gwamnati, Dare Bejide; tsohon kwamishinan yada labarai, Hon. Akinbowale Omole; da kuma tsohon kwamishina, Cif Segun Akinwumi.
Akwai kuma tsohon shugaban ma’aikata ga tsohon gwamna Ayodele Fayose, Cif Dipo Anisulowo; tsohon shugaban SDP a jihar, Dele Ekunola; tsohon dan takarar gwamna, Kayode Adaramodu da wasu tsofaffin ‘yan majalisar wakilai.
An mika katin shaidar zama mamban ADC a hukumance ga Eleka da Omole da sauran shugabannin jam’iyyar, yayin da sauran sababbin mambobi za su karɓi nasu a mazabunsu.
Haka kuma, an bayyana Hon. Omolayo Ilesanmi da Hon. Dare Adekolu a matsayin shugaba da mataimakin shugaban ADC a jihar.
'Atiku ne zai zama dan takarar ADC' - Ayodele
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban cocin INRI Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana hasashensa kan wanda jam’iyyar ADC, za ta ba tikiti a 2027.
A cewarsa, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ne zai lashe tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar hadakar.
Primate Ayodele ya kore yiwuwar jam'iyyar ADC ta tsayar da daya daga cikin su Rotimi Amaechi, Peter Obi ko Nasir El-Rufai a matsayin dan takararta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


