Ana Fargabar El Rufai, Peter Obi na Iya Ficewa daga Hadaka saboda Burin Atiku

Ana Fargabar El Rufai, Peter Obi na Iya Ficewa daga Hadaka saboda Burin Atiku

  • Rikicin cikin gida da ke ci gaba da kunno kai a jam’iyyar ADC na barazana ga karfi da hadin kan 'ya'yanta tun kafin zaben 2027 ya karato
  • Burin Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 a ƙarƙashin ADC ya janyo sabani tsakanin wasu da ke cikin tafiyar hadaka
  • Wasu na ganin Atiku zai shiga ADC don cimma muradinsa kawai, yayin da Nasir El-Rufai ya dage cewa a ba dan Kudu tikiti a zaben 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Alamomi na nuna cewa jam’iyyar ADC na fuskantar rikice-rikice a cikin gida, tun ma ba a kai ga shiga shekarar zabe ta 2027 ba.

An ce da dama daga cikin wadanda suka kafa hadaka na nuna rashin goyon baya ga tsare-tsaren ADC, wanda hakan na iya rage karfinta a 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

Ana zargin El-Rufai, Obi na iya barin ADC saboda burin Atiku na yin takara a 2027
Yayin da Atiku da Obi suka bayyana burin yin takara a ADC, El-Rufai ya ce a kai tikiti Kudu. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

2027: El-Rufai na adawa da burin Atiku

Na gaba-gaba a wannan rikicin shi ne shirin Alhaji Atiku Abubakar, na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, kamar yadda rahoton Business Day ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni da jaridar ta samo na cewa wasu manyan jiga-jigan hadaka, ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ba sa goyon bayan burin Atiku na sake tsayawa takarar shugaban kasa.

El-Rufai dai wanda ya goyi bayan ‘dan Kudu a zaben 2023, yana ci gaba da jaddada cewa Kudancin Najeriya ne ya kamata ta ci gaba da mulkin kasa har zuwa 2031.

El-Rufai zai goyi bayan dan takara daga Kudu

Amma burin Atiku na son yin takara ya janyo rarrabuwar kai a ADC, inda wasu ke ganin shiga jam’iyyar da zai yi ba don ci gaban jam’iyyar ba ne, illa kawai don ya cimma burinsa na zama shugaban kasa a 2027.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sauka, Yilwatda ya hau: Jerin shugabannin APC 9 daga 2013 zuwa 2025

Ba a bayyana ainihin wanda El-Rufai ke goyon baya ba a zaben shugaban kasa na 2027, sai dai majiyoyi daga cikin ADC na cewa ya ce zai goyi bayan dan takara daga Kudu ne kawai.

Legit Hausa ba ta iya tabbatar da wannan ikirari na jaridar cewa El-Rufai ya fito ya bayyana kin amincewarsa da burin Atiku Abubakar ba.

A yanzu dai, Rotimi Amaechi da Peter Obi (dan takarar jam’iyyar LP a 2023) ne suka bayyana sha’awarsu na tsayawa takarar shugabancin kasa daga Kudancin Najeriya.

Wata majiya daga ADC ta ce burin Atiku na yin takara a 2027 na barazana ga jam'iyyar
Atiku, El-Rufai, Amaechi, Aregbesola, Mark da sauran jiga-jigan adawa sun kaddamar da ADC. Hoto: @atiku
Source: Facebook

Burin Atiku zai ruguza jam'iyyar ADC

Wani mamba na rikon kwaryar jam’iyyar ADC ya shaida wa jaridar cewa:

“Burin tsohon mataimakin shugaban kasa yana barazana ga hadin kan jam’iyyar, sai dai idan ya janye niyyarsa.
“Ina tabbatar maka da cewa kowa na fatan ganin sabuwar hadakar siyasa da za ta bai wa 'yan Najeriya damar zaben shugabanni na kirki a 2027, amma idan Atiku ya dage sai ya tsaya takara, to hakan na iya lalata damar da muke da ita."

A cewar jami’in ADC din, jam’iyyar ba za ta hana Atiku tsayawa takara ba, amma za a tabbatar da adalci da daidaito ga duk masu sha’awar tsayawa takara a 2027.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso na tsaka mai wuya a siyasa tsakanin shiga APC, PDP ko ADC,'

An maka shugabannin jam'iyyar ADC a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugabannin ADC daga jihohi biyar sun maka David Mark da wasu a kotu, bisa zargin kwace jam’iyyar ta hanyar kutse da karya doka.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Dumebi Kachikwu, ya ce ana bai wa shugabannin ADC na jihohi cin hancin har N20m domin su sauka daga mukamansu cikin sauki.

A wasu lokuta a baya, jam’iyyar ADC ta kuma zargi jam’iyyar APC da hannu a wata shari’ar da wasu ke yi da sunan mambobin ADC, ba tare da izinin jam’iyyar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com