'Kungiyoyi na Tururuwa zuwa INEC, Masu Neman Zama Jam'iyyu Sun Kai 144

'Kungiyoyi na Tururuwa zuwa INEC, Masu Neman Zama Jam'iyyu Sun Kai 144

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta ce kungiyoyi 10 sun shiga jerin masu sha’awar zama jam’iyyu, wanda ya kai adadin zuwa 144
  • Hukumar, ta bakin shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri'a, Sam Olumekun ne ya bayyana haka da sauran shirin da ake yi
  • Olumekun ya ce INEC ta kaddamar da sabuwar manhajar rajistar jam’iyyu wanda jami'anta suka samar da zimmar sauƙaƙa wa kowa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da kaddamar da sabuwar manhajar rajistar sababbin jam’iyyu.

Wannan mataki na zuwa ne bayan hukumar INEC ta karɓi karin takardun neman rajista daga kungiyoyi guda 10 da ke son zama cikakkun jam'iyyun siyasa.

Ana kara neman rajista a hukumar INEC
INEC ta ce kungiyoyi 10 sun nemi zama jam'iyyu Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa wannan ƙari ya kawo yawan masu neman rajista domin zama jam'iyyun siyasa zuwa 144 a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

INEC: Kungiyoyi na son zama jam'iyyun siyasa

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a, Sam Olumekun, ya bayyana cewa hukumar zaɓe ya tabbatar da karɓar takardun.

Ya bayyana cewa hukumar na nazarin takardun neman rajista da ta karɓa don tantance wacce kungiya ta cika sharuddan da za ta iya neman zama jam'iyya.

Olumekun ya kara da cewa:

“Hukumar na nazarin dukkanin takardun sha’awar neman zama jam'iyya da ta karɓa domin tantance wacce kungiya ce ta cika sharudda don shiga matakin neman rajista kai tsaye. Za mu gabatar da rahoto a taronmu na gaba."

Hukumar INEC ta gina manhajar rajistar jam'iyyu

INEC ta bayyana cewa sashen fasaha da sadarwa (ICT) na hukumar ya tsara tare da kammala aikin gina wannan sabuwar manhaja ta rajista.

Masu son zama jam'iyyun siyasa sun haura 100
INEC na ƙoƙarin tantance masu son zama jam'iyyun siyasa Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Hukumar ta ce:

“A cikin sanarwarmu ta baya, mun tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa mun kammala dukkannin gwaje-gwaje da suka kamata a kan manhajar da muka gina. Wannan sabuwar hanya za ta inganta yadda ake gudanar da rajistar jam’iyyu."

Kara karanta wannan

APC tana neman Sanatoci 2 domin cin karenta babu babbaka a Majalisar dattawa

Olumekun ya kara da cewa cikakken bayani game da sababbin masu neman zaman jam'iyyu, da ya haɗa da sunayensu, lakabi, tambari, adireshi da jagororin riƙo na nan a shafin jam'iyyar.

Ya ce:

“Za mu ci gaba da sanar da ’yan Najeriya duk wani sabon cigaba da muke samu."

Kungiyoyi ne neman rajista da INEC

A baya, mun ruwaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa yawan ƙungiyoyin da ke neman rajista a matsayin jam’iyyun siyasa ya kai 122.

Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da INEC ta fitar a ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025, inda ta bayyana cewa ta karɓi buƙatun kungiyoyi 110 da ke sha’awar zama jam’iyyu a Najeriya.

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Sam Olumekun, da ya tabbatar da haka ya ce ana ci gaba da ƙarbar bukatun jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng