Jam'iyyar PDP Ta Haƙura da Kano, Ta Sauya Wuri da Ranar Gudanar da Babban Taron Ƙasa
- Jam’iyyar PDP ta sauya wuri da lokacin gudanar da babban taron zaben shugabanninta na kasa, inda ta mayar da shi zuwa Ibadan
- Bayan dage taron daga Agusta zuwa Nuwamba, PDP ta ayyana cewa ta warware rikice-rikicenta tare da fatan komawa mulki a 2027
- PDP ta umurci NWC da ta gurfanar da ‘yan siyasar da suka sauya sheka bayan lashe zaɓe a jam’iyyar bisa tanadin tsarin mulki na kasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Asabar, 15 ga Nuwambar 2025, jam’iyyar PDP ta tsayar da rana da wurin da za ta gudanar da babban taronta na kasa.
PDP ta amince cewa za ta gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar na kasa a ranar Asabar, 15 ga Nuwamba 2025 zuwa Lahadi, 16 ga Nuwamba, 2025.

Source: Twitter
PDP ta sauya wurin babban taron kasa
Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya sanar da cewa jam'iyyar ta sauya wurin gudanar da taron zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Debo Ologunagba ya bayyana hakan ne yayin da yake karanta wata takardar bayan taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) da PDP da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.
Da yake karanta takardar bayan taron, Ologunagba, ya ce za a kammala duk shirye-shiryen taron a taron NEC na gaba da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025.
Tun da fari an tsayar da Agustar 2025 matsayin watan gudanar da taron, amma aka dage zuwa Nuwamba, sannan aka sauya wurin taron daga Kano zuwa Ibadan.
PDP na kokarin hade kan mambobinta
Ya ƙara da cewa an umarci shugaban jam’iyyar na ƙasa da sakataren jam’iyyar na ƙasa da su sanar da INEC game da shirin taron zabukan.
Punch ta rahoto NEC ta amince da mambobin kwamitin shirya taron da kuma kwamitin rabon mukamai (ZC) domin tabbatar da sahihin tsarin zaɓe.
Ologunagba ya ce shugabannin jam’iyyar sun nuna gamsuwa da yadda aka warware wasu rikice-rikicen cikin gida, wanda ya nuna cewa PDP ta jajirce wajen dawo da haɗin kai.
Ya ƙara da cewa PDP na nan daram da haɗin kai, kuma za ta ci gaba da zama madogara mai inganci ga al’ummar Najeriya, da nufin karbar mulki daga APC a 2027.

Source: Twitter
Za a yi karar ’yan siyasa da suka sauya sheƙa
A wani muhimmin ɓangare na ƙudurorin, NEC ta umarci Kwamitin Gudunarwa na Ƙasa (NWC) da ya fara shirin gurfanar da tsoffin mambobin PDP da suka lashe zaɓe amma suka koma wasu jam’iyyu.
A cewar sanarwar:
“A ƙoƙarinta na kare amanar ’yan Najeriya da suka zabi PDP, NEC ta umurci NWC da ya dauki matakin doka domin kwato kujerun dukkanin 'yan majalisar tarayya da na jihohi da suka lashe zaɓe a jam’iyyar PDP amma suka sauya sheka.
“Dangane da sashe na 68 (1)(g) da kuma 109 (1)(g) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wadannan mambobin sun rasa kujerunsu."
2027: PDP ta fara neman dan takara tun yanzu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, waɗanda suka kafa PDP a 1998 sun bayyana matsayarsu kan wanda ya kamata a tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027.
A wani taro da suka gudanar a Abuja, jiga-jigan PDP sun amince a ɗauko ɗan takara a Kudancin Najeriya domin tabbatar da adalci da daidaito.
Farfesa Jerry Gana ya caccaki gwamnatin APC da cewa ta kawo talauci dabrashin tsaro maimakon alkawarin da ta yi na kawo canji a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

