'Zan Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2027 idan Peter Obi Ya Janye,' Inji Datti Baba Ahmed
- Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ce zai tsaya takarar shugaban ƙasa ne kawai idan wasu mutum biyu da yake darajarsu suka ki tsayawa a 2027
- A cewarsa, har yanzu ba ya da tabbacin barin jam’iyyar LP ko komawa ADC duk da gamayyar jam’iyyun adawa da ke kokarin haɗa kai
- Ya ce yana so Peter Obi ya sake tsayawa takara a 2027 kuma zai mara masa baya, sai dai idan wasu da yake girmamawa sun ƙi shiga takara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon abokin takarar Peter Obi, dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya yi magana kan zaben 2027.
Datti Baba Ahmed ya ce zai shiga takarar shugabancin ƙasa a 2027 ne kawai idan wasu mutum biyu da yake matuƙar girmamawa suka ki shiga takarar.

Kara karanta wannan
Ana neman haɗa Atiku da Peter Obi faɗa bayan 'gano' wanda ADC ke shirin ba takara a 2027

Asali: Twitter
Jam'iyyar LP na cikin rikicin shugabanci
A wata hira da aka yi da shi a tashar Arise News a ranar Talata, 22 ga Yuli, Baba-Ahmed ya bayyana cewa bai yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027 ba tukuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Litinin, 21 ga Yuli, Datti Abba Ahmed ya gana da bangaren jam’iyyar LP da Barista Julius Abure ke jagoranta.
A halin yanzu jam’iyyar LP na fama da rikicin shugabanci wanda ya haifar da ɓangarori biyu: daya ƙarƙashin Abure, ɗaya kuma ƙarƙashin tsohuwar ministar kuɗi Usman Nenadi.
Datti Baba-Ahmed ba zai bar LP zuwa ADC ba
A wajen taron, Datti ya bayyana ra’ayinsa kan sabuwar gamayyar jam’iyyun adawa da aka kafa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ADC.
Ya ce yana ganin mafi yawan 'yan gamayyar — ciki har da Peter Obi, Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, David Mark da wasu tsofaffin gwamnoni — na da burin takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
ADC: Atiku da El Rufai sun fara fuskantar abin da ba su yi tsammani ba daga manyan Arewa
Baba-Ahmed ya ce:
“Ra’ayina shi ne, sai an bani hujja mai karfi da zai sa in bar LP in koma ADC. Har yanzu babu wanda ya gamsar da ni da hakan. Ina so Peter Obi ya samu tikitin jam’iyyar LP a 2027, ko da tare da ni ko ba tare da ni ba.”

Asali: Twitter
"Ba ni da burin tsayawa takara" - Datti
Yayin ci gaba da bayani a hirar, Datti Baba-Ahmed ya musanta jita-jitar da ke cewa yana shirin barin Peter Obi ko jam’iyyar LP, inda ya ce:
“Wasu mutane suna furta tsoronsu, amma ba gaskiya ba ne. Ban faɗi hakan ba. Akwai shaidu na bidiyo daga dukkan tattaunawa da aka yi – ban ce hakan ba.”
Ya ƙara da cewa:
“Na mara wa Peter Obi baya da zuciya ɗaya, kuma zan sake yi a 2027. Sai dai idan wasu mutum biyu da nake girmamawa suka ki tsayawa takara, kuma Allah ya ba ni dama, shi ne kawai sai na fito takara, amma idan ba haka ba, to zan sake tsayawa tare da Peter Obi.
"Idan bai tsaya ba, to akwai wani mutum daga Kudu da nake so ya tsaya, wanda ba zan fadi sunansa ba. Amma ban da wani burin tsayawa takara. Manyan burina su ne: 'A dakatar da kashe-kashe', 'a dakatar da sata'.”
Kalli bidiyon tattaunawar a kasa:
"Za ka yi mummunar faduwa" - Datti ga Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, abokin takarar Peter Obi a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya janye niyyar neman wa’adi na biyu.
Datti ya ce idan har Tinubu na da hangen nesa da kwarewar siyasa kamar yadda mutane ke cewa, bai kamata ya sake tsayawa takara a 2027 ba.
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar LP ya bayyana cewa alamu sun nuna APC za ta fuskanci mummunan rashin nasara a zaɓe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng