ADC: Atiku da El Rufai Sun Fara Fuskantar Abin da ba Su Yi Tsammani ba daga Manyan Arewa
- Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya juyawa haɗakar adawa baya, ya bayyana cewa yana nan daram a jam'iyyar PDP
- Ortom, wanda ya ayyana kansa da jagoran PDP a Benuwai, ya yi ikirarin cewa haɗakar su Atiku, Obi da El-Rufai ba za ta kai labari ba
- Ya ce ba zai shiga jam'iyyar ADC ba domin ya san jam'iyyar ba za ta kai ko'ina ba za a tumurmusa ta a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Jagororin haɗakar adawa, Atiku Abubakar da Malam Nasiru El-Rufai sun fara fuskantar tirjiya daga jagororin Arewa da suka yi tsammanin za su goyi bayansu.
Tsohon Gwamnan Jihar Benuwai a Najeriya, Samuel Ortom, ya ce ba zai shiga jam’iyyar haɗakar adawa watau ADC ba.

Source: Facebook
Samuel Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2025 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Samuel Ortom ya nesanta kansa da shiga ADC
Ya ce kowane ɗan ƙasa na da ’yancin shiga duk irin kawancen da ya ga dama, amma shi da mabiyansa za su ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar adawa ta PDP.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana kansa a matsayin jagoran PDP a jihar Benuwai, yana mai cewa shi da waɗanda yake jagoranta ba za su shiga ADC ba.
“Kowa na da ’yancin shiga kowace haɗaka da ya ke so, amma ni da mutanen da nake jagoranta, za mu ci gaba da kasancewa a PDP.
"Ni ne jagoran PDP a Jihar Benuwai, kuma mamba a Majalisar amintattu na kasa (BoT); ba zan shiga wata kawance ba. Ba mu da wata alaka da hakan.”
- Inji Samuel Ortom.
Ortom ya hango faɗuwar ADC
Tsohon gwamnan ya ce bai yarda cewa wannan tafiya da jam’iyyar ADC ke jagoranta za ta iya jure matsin lambar siyasa ba.
Ya kara da cewa ko da jam’iyyar ta ci nasarar shawo kan matsalolinta na kotu, za a kayar da ita a gaban akwatin zaɓe.
"Ba na ganin za su tsallake, ko da sun tsira daga shari’ar da ake yi yanzu, za a kayar da su ba tare da wahala ba,” inji shi.

Source: Facebook
Ficewar Atiku daga PDP ta taɓa Ortom?
Ortom ya ce bai yi mamakin ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar daga PDP ba, kamar yadda The Cable ta kawo.
Atiku, wanda yana daga cikin wadanda suka kafa PDP tun farko, ya fice daga jam’iyyar a makon da ya gabata, kuma ana sa ran zai shiga ADC a hukumance nan ba da jimawa ba.
Samuel Ortom ya ce tafiyar Atiku ba abin mamaki ba ce, domin idan aka duba tarihi, ya saba sauya sheƙa daga wannan jam'iyya zuwa waccan.
Ortom ya ce babu tsama tsakaninsa da Buhari
A wani rahoton, kun ji cewa Samuel Ortom ya musanta zargin vewa yana da tsama da tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
Tsohon gwamnan na daga cikin gwamnoni a wancan lokaci da suke sukar gwamnatin tarayya wanda marigayi Buhari ke jagoranta.
Ortom ya ce bai tsani Buhari ba kamar yadda ake zargi amma ya ya tabbatar da cewa ya rika suƙar salon marigayin wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar Benuwai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


