'Za Mu iya Aiki Tare,' Abin da Kwankwaso Ya Fada bayan Haduwa da Tinubu a Aso Villa

'Za Mu iya Aiki Tare,' Abin da Kwankwaso Ya Fada bayan Haduwa da Tinubu a Aso Villa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a wani zama na sirri da aka yi a gidan shugaban ƙasa
  • Ganawar na zuwa ne jim kadan bayan da Kwankwaso ya halarci taron tattalin arzikin daji da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa
  • Kwankwaso na ci gaba da jan hankalin 'yan adawa da ke ƙoƙarin haɗa kawunansu don kalubalantar APC a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, a wani zama na sirri da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa.

Ganawar ta faru ne a ranar Litinin bayan fitowar Kwankwaso a wajen taron da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Ana rade radin zai shiga jam'iyyar APC, an hango Kwankwaso a fadar shugaban kasa

Haduwar Kwankwaso da Tinubu a 2023. Hoto: Bayo Onanuga
Haduwar Kwankwaso da Tinubu a 2023. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa wannan shi ne karo na biyu da aka samu ganawa tsakanin shugaba Tinubu da Kwankwaso cikin fiye da shekara biyu, tun bayan zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya gana da Tinubu a Aso Villa

Rahotanni sun bayyana cewa ganawar ta faru ne a gidan shugaban ƙasa, inda ba a bai wa ‘yan jarida damar halarta ba, kuma babu wani bayani kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa.

Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa manema labarai cewa ganawar ta gudana ne ba tare da yawancin hadiman shugaban ƙasa ba.

Majiyoyi sun ce har yanzu ba a bayyana takamaiman abin da aka tattauna ba, amma ana danganta wannan ganawa da ƙoƙarin gyara dangantaka ko shirin haɗin gwiwa.

Rabiu Kwankwaso ya ce ya tattauna da shugaba Tinubu kan batutuwan da suka shafi siyasa, inda ya bayyana yiwuwar yin aiki tare da shugaban ƙasa, duk da bai fadi wane irin aiki ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya isa fadar shugaban kasa taron da ake sa ran Tinubu zai halarta

Haduwar Tinubu da Kwankwaso a 2023

Ganawar da suka yi a jiya ba ita ce ta farko ba, domin a ranar 9 ga Yuni, 2023, makonni bayan rantsar da shugaban ƙasa, Kwankwaso ya ziyarci Aso Villa.

Rahotanni sun bayyana cewa a wancan lokacin, shugabannin sun tattauna kan harkokin siyasa da shugabanci.

Tattaunawarsu ta baya na ɗaya daga cikin alamu da ke nuna irin dangantakar da ke tsakaninsu duk da bambancin jam’iyya da ra’ayi a harkar siyasa.

Jam'iyyun adawa na zawarcin Kwankwaso

Ko da yake ba a bayyana matsayin Kwankwaso kan wannan ganawa ba, ganawar na zuwa ne makonni bayan da jam’iyyar ADC ta sanar da ƙaddamar da hadaka.

Kwankwaso, wanda ya kafa tafiyar Kwankwasiyya, na ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasa daga Arewacin Najeriya, kuma yana da ƙarfi a Kano.

A 2023, jam’iyyarsa ta NNPP ta lashe kujerar gwamna da mafi yawan kujerun majalisar dokokin jihar Kano, alamar da ke nuna tasirin Kwankwaso a jihar da ma Arewacin ƙasa.

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

Lokacin da Kwankwaso ya ziyarci fadar shugaban kasa
Lokacin da Kwankwaso ya ziyarci fadar shugaban kasa. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Duk da cewa jam’iyyar NNPP ba ta cikin sabuwar kawancen da ADC ke jagoranta, wasu jiga-jigan adawa na zawarcin Kwankwaso domin haɗa kai da shi a shirin karɓe mulki daga APC.

Kwankwaso ya yi wa iyalan Buhari jaje

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ta'aziyya gidan marigayi Muhammadu Buhari.

Kafin zuwa gidan, Kwankwaso ya tsaya a fadar mai martaba Sarkin Daura ya masa ta'aziyyar rashin da aka musu.

Madugun Kwankwasiyya ya yi addu'a tare da rokon Allah ya gafarta wa shugaba Muhammadu Buhari da ya riga mu gidan gaskiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng