Tsohon Sakataren Gwamnati da Ke Harin Kujerar Gwamna Ya Fice daga PDP a Jihar Bauchi

Tsohon Sakataren Gwamnati da Ke Harin Kujerar Gwamna Ya Fice daga PDP a Jihar Bauchi

  • Tsohon sakataren gwamnatin Bauchi, Barista Ibrahim Kashim, ya fice daga jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ba tare da bayyana dalili ba
  • Ya nuna godiya ga shugabannin PDP da suka ba shi dama ya zama ɗan takarar gwamna a 2023 kafin ya janye wa Gwamna Bala Mohammed
  • Bayan ficewa daga PDP da gwamnatin Bala a Janairu, rahoto ya nuna cewa Kashim na iya tsayawa takarar gwamna a 2027 a wata jam’iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Tsohon sakataren gwamnatin Bauchi kuma ɗan takarar gwamna a zaben 2023, Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ya fice daga PDP.

Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya sanar da yin murabus daga zama mamba PDP ne a wasikar da ya aikawa shugaban PDP na mazabar Majidadi, jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

PDP ta yi rashi, tsohon daraktan kungiyar gwamnoni ya koma ADC

Tsohon sakataren gwamnan Bauchi ya yi murabus daga jam'iyyar PDP
Barista Ibrahim Muhammasd Kashim, tsohon sakataren gwamnatin Bauchi ya bar PDP. Hoto: Abdul-Hadee Isah Ibraheem
Source: Facebook

Tsohon sakataren gwamnatin Bauchi ya bar PDP

Jaridar The Nation ta samu wasikar a ranar Litinin, inda a ciki aka ga Barista Kashim bai bayyana dalilin ficewarsa daga jam’iyyar ta PDP ba.

Sai dai tsohon sakataren gwamnatin ya yi godiya ga PDP da kuma jagororin mazabarsa bisa yarda da damar da suka bashi don yiwa jam'iyyar hidima.

Wasikar ta nuna cewa Barista Kashim ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance tun daga ranar da aka rubuta wasikar, watau 21 ga watan Yulin 2025.

“Bayan yin dogon nazari da tattaunawa mai zufi, ina so in sanar da ku a hukumance cewa daga yau, na yi murabus daga mamban jam’iyyar PDP.
"Zan ci gaba da neman hanyoyin da suka fi dacewa da ni, wadanda za su ba ni duk wata dama ta yi wa al'umma hidima cikin aminci, gaskiya, ƙwazo, da tsoron Allah.”

- Barista Ibrahim Muhammad Kashim.

Siyasar Barista Kashim a zaben 2023

Kara karanta wannan

'Zai dawo': PDP ta yi watsi da ficewar Atiku, ta faɗi babban abin da zai dawo da shi

Barista Kashim ya nuna godiya ta musamman ga shugabannin mazabarsa da suka ba shi damar zama mamba mai daraja a cikin jam'iyyar PDP.

Ya ce a cikin jam'iyyar ne ya samu tikitin takarar kujerar gwamnan Bauchi a zaɓen 2023 kafin daga bisani ya janyewa Gwamna Bala Mohammed bayan ya fadi a takarar shugaban ƙasa.

Ya ce duk da kasancewarsa sakataren gwamnati, ya zaga kananan hukumomi a fadin jihar domin tallafawa yakin neman zaben Gwamna Bala.

An ce tsohon sakataren gwamnatin Bauchi ya ajiye aikinsa a Janairu ne bisa umarnin Gwamna Bala Mohammed
A 2023 ne Barista Ibrahim Kashim ya janye daga takarar gwamna, ya ba Gwamna Bala Mohammed. Hoto: Mukhtar Gidado
Source: Facebook

Akwai yiwuwar Kashim ya nemi gwamna

A cewarsa, ya yi uwa ya yi madaukiya don ganin nasarar Gwamna Bala, musamman ganin irin ƙalubalen da ‘yan takarar wa’adi na biyu ke fuskanta a tarihin siyasar jihar Bauchi.

Mun rahoto cewa Barista Kashim ya koma kujerarsa a matsayin sakataren gwamnati har zuwa watan Janairu 2025, lokacin da ya ajiye aikinsa bisa umarnin gwamnan.

Kodayake bai bayyana matakin da zai dauka na gaba ba, rahotanni daga Daily Trust na nuna cewa akwai yiyuwar ya sake shiga takarar gwamna a 2027 a wata sabuwar jam’iyya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Atiku, ya fice daga jam'iyyar PDP

Gwamna ya sake nada Kashim sakatare

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamna Bala Mohammed ne ya lashe zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan Bauchi karkashin jam’iyyar PDP a ranar Asabar, 4 ga Yuni, 2022.

Zaben ya biyo bayan janyewar Barista Ibrahim Muhammad Kashim, wanda ya lashe zaben farko, domin bai wa Gwamna Bala dama ya sake tsayawa takara.

Bayan janyewa daga takarar gwamna, Gwamna Bala Mohammed ya mayar da Barista Ibrahim Kashim kan kujerarsa ta sakataren gwamnatin jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com