2027: Jigon NNPP Ya ba Kwankwaso Shawara kan Takara da Tinubu

2027: Jigon NNPP Ya ba Kwankwaso Shawara kan Takara da Tinubu

  • Tsohon ɗan takarar gwamna a Jigawa, Aminu Ringim ya bayyana muhimmancin Rabi'u Musa Kwankwaso a zaben 2027
  • Ya ce yanzu Najeriya ta kai matakin da ya kamata a nemi Sanata Kwankwaso ya kawo mata ɗauki domin ceto rayuwar jama'a
  • Malam Ringim, ya ce duk wanda ya yi aiki da Kwankwaso, ya san baya wasa da dukiyar talakawan da ya ke jagoranta ta kowace fuska

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani jigo a jam’iyyar NNPP kuma dan takarar gwamna a jihar Jigawa a zaben 2023, Malam Aminu Ringim, ya yi magana kan zaɓen 2027.

Ya bukaci jagoran Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya sake fitowa takarar shugaban kasa a babban zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

Yadda yan PDP ke rokon Kwankwaso, Abba su sauya sheka a Kano

Bola Tinubu da Rabi'u Musa Kwankwaso
Ana son Kwankwaso ya yi takara da Tinubu Hoto: Bayo Onanuga/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Nigerian Tribune ta wallafa cewa Ringim ya ce Kwankwaso ne kadai dan siyasar da ke da kishin ƙasa da gogewar da ake buƙata don ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta.

Ringim ya fadi muhimmancin takarar Kwankwaso

Tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa, Malam Aminu Ringim ya ce lokaci ya wuce da za a riƙa laluben ƴan siyasa da za su ceto Najeriya.

A kalamansa:

Saboda Najeriya ba za ta iya jira ba. Mun kai ga wani yanayi mai haɗari ta tattalin arziki da kuma ta tsaro."
"A cikin dukkanin manyan ‘yan siyasa da mu ke da su a yau, babu wanda ya hada hangen nesa, kwarewa da kishin kasa irin na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.”

Ya kafa da cewa Kwankwaso ɗan kishin ƙasa ne da ke da muradin ceto Najeriya da inganta rayuwar jama'a, ba wai kawai ƙwadayin mulki ba.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Ana ganin Kwankwaso ne kawai zai iya ceto Najeriya Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Malam Aminu Ringim ya ce:

Kara karanta wannan

"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

Abin da muke bukata yanzu shi ne jagora da aka riga aka gwada, mai kuzari da kuma kishin kasa ba tare da wata rufa-rufa ba."
"Wannan ne dalilin da ya sa muke kira gare shi – a madadin miliyoyin ‘yan Najeriya – da ya amsa kiran, ya jagoranci Najeriya a 2027."

Ringim: "Mun san aikin Kwankwaso"

Ringim ya yaba da ayyukan Kwankwaso a lokacin da yake gwamna, musamman a bangaren ilimi, raya matasa da kuma gine-gine da suka kawo ci gaba a Kano.

Ya ce:

"A Kano, ya sauya fannin ilimi, ya tallafawa matasa, ya sabunta abubuwan more rayuwa, kuma ya gina tsarin mulki da ya faranta wa mutane rai,”

Game da cin hanci, Ringim ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagora mai tsattsauran ra’ayi kan gaskiya da riƙon amana.

Ya ce:

“Kwankwaso ba ya sassaucta wa cin hanci. Ka tambayi duk wanda ya taba aiki da shi. A duk lokacin mulkinsa a Kano, an san shi da cikakken tsari kan kudi. Kowane kwabo an san inda ya tafi."
"Bai taba amfani da dukiyar jama’a don kansa ba, bai yarda da ‘yan amshin shata ko ɓarayi a kusa da shi ba. "

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya tsage gaskiya kan batun Kwankwaso zai koma ADC

An roki Kwankwaso, Abba su shiga PDP

A baya, kun ji cewa wata jigo a PDP reshen jihar Kano, Hon. Zainab Audu Bako, ta bayyana irin fatan da wasu 'yan jam’iyyar ke yi wa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Hon. Zainab ta roƙi Injiniya Abba Kabir Yusuf, da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da su gaggauta dawo wa jam’iyyar PDP saboda amfanin hakan.

Zainab Audu Bako ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ita ce mafita ta siyasa ga Gwamna Abba da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng