Atiku Ya Buɗe Ƙofa, Sanata na 2 Ya Fice daga Jam'iyyar PDP a Ƙasa da Awanni 24

Atiku Ya Buɗe Ƙofa, Sanata na 2 Ya Fice daga Jam'iyyar PDP a Ƙasa da Awanni 24

  • Kwanaki kaɗan bayan Atiku Abubakar ya yi murabus, Sanatan Osun ta Tsakiya, Olubiyi Fadeyi ya fice daga jam'iyyar PDP
  • Sanatan ya zama na biyu a ƙasa da sa'o'i 24 da ya bar jam'iyyar PDP a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
  • A wasiƙar da ya aikawa shugaban PDP na mazaɓarsa mai ɗauke da kwanan watan 12 ga Yuli, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin cikin gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Sanata mai wakiltar Osun ta Tsakiya a majalisar dattawa, Olubiyi Fadeyi, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.

Fadeyi ya aika da wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan wata 12 ga Yuli, 2025, zuwa ga Shugaban PDP na mazaɓa ta 3, da ke Oke Ejigbo, Ila Orangun, a jihar Osun.

Kara karanta wannan

PDP ta kara birkicewa, babban sanata ya yi murabus daga jam'iyyar

Sanatan Osun ta Tsakiya, Olubiyi Fadeyi.
Jam'iyyar PDP ta rasa sanata na 2 cikin awanni 24 a jihar Osun Hoto: Ajagunla Olubiyi Fadeyi
Source: Facebook

Sanata Fadeyi ya tabbatar da sahihancin wasiƙar a wani saƙo da ya aika wa wakilin jaridar Punch a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli, 2025, bayan kwafinta ya shiga hannun ƴan jarida.

Me yasa Sanata Fadeyi ya bar PDP?

A wasiƙar, Sanatan ya ce:

“Ina mai sanar da ku a hukumance cewa na fice daga jam’iyyar PDP daga yau, ba tare da ɓata lokaci ba.
"Rigingimu da rabuwar kai da har yanzu aka gaza warware wa tsawon shekaru a matakin ƙasa da yawan kai ƙara kotu ne ya sa na yanke shawarar fita daga PDP.
"Kuma sai da na nemi shawarwari daga abokan siyasa, makusanta da iyalai na kafin na yanke hukuncin barin jam'iyyar."

Sanata na 2 ya fice daga PDP a Osun

Tun farko, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, shi ma ya fice daga jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Atiku, ya fice daga jam'iyyar PDP

Fadahunsi, wanda ya yi wa’adi biyu a majalisar dattawa, ya bayyana cewa sabani da rikice-rikicen shari’a da suka daɗe ba a warware ba ne suka tilasta masa ɗaukar wannan mataki, rahoton The Nation.

Majalisar Dattawan Najeriya.
Jam'iyyar PDP ta rasa sanatoci 2 cikin awanni 24 a Osun Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

A wani ɓangare na wasiƙar da ya sa hannu a kai wacce aka aikawa Shugaban PDP na Mazaba ta 4 kuma mai ɗauke kwanan wata 12 ga Yuni, 2025, ya ce:

"Ina mai sanar da ku a hukumance cewa daga yau na fice daga jam’iyyar PDP sakamakon sabani da rashin jituwar da aka gaza gyarawa da kuma dogon rikicin shari’a da suka dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023."

Wannan dai ya nuna cewa jam'iyyar PDP ta rasa Sanatoci biyu a cikin ƙasa da awanni 24 a jihar Osun, sai dai har yanzu ba su bayyana jam'iyyar da za su koma ba.

Gwamnan Osun na shirin raba gari da PDP

A wani labarin, kun ji cewa jita-jitar da ake yaɗawa cewa gwamnan Osun, Ademola Adeleke zai sauya sheƙa daga PDP zuwa APC ta ƙara karfi.

Fitaccen mawakin nam Davido ya fitar da wata sabuwar waƙa da ke nuna kawun nasa watau Gwamna Adeleke na shirin komawa inuwar tsintsiya.

Mawakin bai iira suna gwamnan ko jam'iyyun PDP da APC ba a baitukan wakar, amma an ji yana ambatar tsintsiya da laima, tambarin manyan jam'iyyun biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262