Sauya Tsarin Mulki: Ana Son Shugaban Kasa Ya Dawo yin Shekara 6 ba Tazarce

Sauya Tsarin Mulki: Ana Son Shugaban Kasa Ya Dawo yin Shekara 6 ba Tazarce

  • Lauyoyi da ‘yan rajin dimokuradiyya na son a takaita wa’adin mulki zuwa guda na shekara shida don hana asarar kudin kamfen
  • Wasu daga cikin masu fafutukar sun ce hakan zai rage amfani da dukiyar jama’a da shugabanni ke yi don sake lashe zabe
  • Sai dai duk da haka, wasu na ganin karin wa’adi ga shugabanni na inganta tsarin aikin gwamnati da fahimtar matsalolin jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu kwararru da masu rajin dimokuradiyya a Najeriya na kira da a gyara kundin tsarin mulki ta hanyar canza tsarin wa’adin shugabanci zuwa daya mai tsawon shekara shida.

A cewarsu, hakan zai rage tashe-tashen hankula da amfani da dukiyar jama’a wajen neman tazarce bayan karewar wa’adin farko, da kuma kawo daidaito a harkokin mulki.

Kara karanta wannan

2027: An shigar da ADC kotu bayan Atiku ya bar PDP, ana son ruguza hadaka

Shugaba Tinubu na jawabi a zauren majalisar wakilai
Shugaba Tinubu yayin jawabi a zauren majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A tattaunawar da Vanguard ta yi da su, sun ce akwai bukatar shugabanni su mayar da hankali wajen yi wa ‘yan kasa aiki, maimakon bata lokaci da dukiya wajen shirye-shiryen tazarce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shekara 6 mai wa’adi 1 ya fi” — Lauya Eromosele

Lauya kuma daraktan gidauniyar Oneghe Sele da ke Benin, Saint Moses Eromosele ya ce Najeriya za ta fi cin gajiyar wa’adi guda na shekaru shida saboda zai sa a yi aiki sosai.

Ya ce tsarin zabe duk bayan shekara hudu ya fi dacewa da kasashen da suka cigaba kamar Amurka.

Amma a Najeriya da ke fama da kalubale, ya ce hakan na gurgunta aiki da kuma haddasa kashe kudi ba ta hanyar da ta dace ba.

“Zai rage dabanci da cin hanci” — Kungiyar Arewa

Shugaban Coalition of Northern Groups (CNG), Jamilu Aliyu Charanchi, ya ce tsarin wa’adi biyu na shugaban kasa da gwamnoni yana kara dabanci da amfani da dukiyar jama’a don cimma tazarce.

Kara karanta wannan

London Clinic: Abubuwan mamaki game da asibitin da Muhammadu Buhari ya rasu

A cewarsa, shugabanni da dama suna barin aiki a wa’adin farko suna shirya tazarce, yayin da wa’adi na biyu ke cike da halin girman kai.

“Zai kawo kwanciyar hankali” — Mutanen Benue

Kungiyoyin kabilu a jihar Benue kamar Mzough U Tiv (MUT), Ochetoha K’Idoma (OKI), da Om Nyi’Igede (ONI), sun bayyana cewa wa’adi daya na shekaru shida zai kawo kwanciyar hankali.

Sun ce hakan zai hana shugabanni su bata lokaci da kudi wajen neman tazarce, kuma zai sa su fi jajircewa wajen yi wa jama’a aiki.

“Zai kara adalci a kasa” — Dickson Sule

Wani mai fafutukar dimokuradiyya, Dickson Sule ya ce tsarin wa’adi daya zai taimaka wajen kara adalci da kuma rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da zabuka.

Ya ce duk shekara hudu sai an sake zabe a Najeriya, wanda ke janyo asarar kudi da kuma gajiyar da INEC da masu kada kuri’a.

“Za a fi mayar da hankali kan aiki” — Isaac Abaa

Kwararre a fannin watsa labarai, Isaac Abaa ya ce wa’adi daya na shekaru shida zai ba shugabanni damar mayar da hankali wajen aiki fiye da kamfen.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari 12 da suka yi amo a Najeriya kuma za su sa a rika tunawa da shi

Ya ce rashin tazarce zai hana amfani da dukiyar gwamnati wajen kamfen, tare da rage gajiya da zabuka ga jama’a da hukumomin zabe.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabion
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabion. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

“Ina adawa da tsarin” — 'Dan APC a Ondo

Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC a Ondo, Hon. Steve Otaloro ya bayyana rashin goyon bayansa ga tsarin wa’adi guda na shekaru shida.

A cewarsa, tsarin wa’adi biyu yana karfafa daukar nauyin al’umma, domin shugabanni na tsoron rasa mukami idan basu yi aiki ba, don haka suke kokarin kyautata shugabanci.

An saya wa Tinubu motocin kamfen

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan majalisar jihar Kebbi sun saye motocin kamfen sama da 20 ga shugaban Bola Tinubu.

Rahotanni sun bayyana cewa sun hada motocin ne domin shirin kamfen din 2027 ga Tinubu da gwamna Nasir Idris.

Sai dai kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa a jihar sun yi Allah wadai da matakin da majalisar Kebbi ta dauka na sayen motocin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng