Bayan Tafiyar Atiku, Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen PDP Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar
- Daraktan yakin neman zaben Asue Ighodalo, dan takarar gwamnan Edo, Matthew Iduoriyekemwen, ya yi murabus daga PDP
- Iduoriyekemwen ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP saboda rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa
- Murabus din daraktan yakin neman zaben na zuwa ne 'yan kwanaki bayan Atiku Abubakar, tsohon dan takarar shugaban kasa ya bar PDP
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Daraktan yaƙin neman zaɓen Asue Ighodalo, dan takarar gwamnan Edo, Matthew Iduoriyekemwen, ya yi murabus daga jam'iyyar adawa ta PDP a ranar Alhamis.
Murabus ɗinsa na kunshe ne a cikin wata wasiƙa mai dauke da kwanan wata 17 ga Yulin 2025, wadda aka aike wa shugaban PDP na Ward 5, karamar hukumar Ikpoba-Okha, jihar Edo, Andrew Esemuede.

Source: Twitter
Dalilin murabus din daraktan Asue Ighodalo
Iduoriyekemwen ya bayyana cewa ya yi murabus daga PDP ne saboda matsalolin da suka turnuke jam'iyyar a matakin jiha da na ƙasa, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasiƙar Iduoriyekemwen ta ce:
"Ina rubuto wannan wasiƙar ne domin na sanar da ku hukuncin da na yanke na ficewa daga jam’iyyar PDP, Ward 5, Ikpoba-Okha LGA, Jihar Edo.”
"Na dauki matakin bayan shawarwari masu zurfi, saboda PDP ta taka muhimmiyar rawa a tafiyata ta siyasa da ci gaban kaina.
"Saboda wannan dalilin, ina matuƙar godiya kuma zan kasance mai godiya da yabawa damarmakin da jam'iyyar ta samar mini.
"Yayin da nake wannan yabawar, a hannu daya kuma, abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar — ko a matakin jiha ko na ƙasa — sun sa ba zan iya ci gaba da kasancewa a cikinta ba.”
"PDP ta sauka daga tafarkinta" - Iduoriyekemwen
Matthew Iduoriyekemwen ya ce ya fahimci cewa jam'iyyar PDP ta sauka daga kan turbar da aka kafata ta asali.
Jaridar Vanguard ta rahoto shi yana cewa:
"Hanyar da aka dauka da kuma tsarin da na ga PDP na tafiya a kansu sun sauka daga gwadaben wadanda iyayenmu suka kafa, da alama tsare-tsaren sun ɓace.
"Abin da muke gani a yau ya sauka kwata-kwata daga irin matakan da shugabannin jam'iyyar na asali suka kafa bisa hangen nesa ba, komai ya fara komawa akasin na demokaraɗiyya.
"Mun daina ganin tsare-tsaren da suke hada kan jama'a, kishin talakawa da kare ra'ayoyin mambobinta wajen yanke duk wani hukunci."

Source: Twitter
"Ba fushi ko zafin rai ba ne" - Iduoriyekemwen
Iduoriyekemwen ya jaddada cewa ba fushi ko zafin rai ne ya sanya shi ficewa daga PDP ba, sai dai don neman tsare mutuncinsa da ƙimomin rayuwarsa.
“Na yanke wannan shawara ne domin in mai da hankali kan iyalina da harkokin kasuwanci.
“Ina mika godiyata ga shugabannin jam’iyya da mambobin Ward 5, karamar hukumar Ikpoba-Okha bisa soyayya da goyon baya da suka bani tsawon shekaru. Ina yi wa PDP fatan alheri a gaba.”
- Matthew Iduoriyekemwen.
Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Atiku Abubakar, ya fice daga PDP, bayan shafe shekaru yana matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Atiku ya bayyana murabus ɗinsa ne a cikin wata wasika da ya sanya wa hannu, wadda aka aike wa shugabannin PDP na ƙaramar hukumar Jada a jihar Adamawa, a ranar 14 ga Yuli, 2025.
Ficewar Atiku daga PDP na zuwa ne a daidai lokacin da hadakar 'yan adawa suka koma jam’iyyar ADC, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


