Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC

Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC

- Mr. Mathew Iduoriyekemwen ya zargi Sanata Shehu Sani da baiwa kwamitinsa cin hancin N10m

- Ya ce Shehu Sani ya gabatar da cin hancin ne da nufin sauya sakamakon zaben fidda gwani na APC da ya gudana a fadin jihar

- Sai dai, Shehu Sani ya mayar da martani akan wannan zargi na Mr. Mathew, yana mai cewa, wannan tsagwaron karya ce kawai ya shirya

Shugaban kwamitin karbar koke koke da jam'iyyar APC ta kafa, bayan kammala zaben fitar da gwani a jihar Kaduna, Mr. Mathew Iduoriyekemwen ya zargi Sanata Shehu Sani da baiwa kwamitinsa cin hancin N10m don tabbatar da shi a matsayin dan takarar sanatan Kaduna ta tsakiya ba tare da abokin hamayya ba.

Sai dai, Shehu Sani ya mayar da martani akan wannan zargi na Mr. Mathew, yana mai cewa, "wannan tsagwaron karya ce kawai ya shirya," tare da yin nuni da cewar ba ya bukatar baiwa kowa cin hanci kafin samun tikitin yin takara a mazabarsa, kuma cikin jam'iyyarsa.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, Mr. Iduoriyekemwen ya fadada zarginsa da cewar Shehu Sani ya gabatar da kudaden cin hancin ne ga kwamitin ta hannun wani mamban kwamitin, da nufin sauya sakamakon zaben fidda gwani na APC da ya gudana a fadin jihar.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria 10,000 ne suka dawo Nigeria daga kasar Libya - NEMA

Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC

Shehu Sani ya bani cin hancin N10m amma naki karba - Shugaban kwamitin zaben APC
Source: Depositphotos

Ya ce, "Mutum daya ne a Kaduna wanda ya bani cin hancin kudi, shine Shehu Sani, ta hannu daya daga cikin mambobin kwamitin da na ke jagoranta, wanda ya sanar dani cewa Sani ya bani wannan N10m a matsayina na shugaban kwamitin. Sai dai tun a lokacin na sanar da su bana bukatar kudinsu.

"Hatta bayan da aka kammala zaben fidda gwanin, kafin bayyana sakamakon zabe, Shehu Sani da wasu mutanensa sun hura mun wuta akan lallai sai na karbi wannan kudi. Sau tari yana kirana, amma kowane lokaci amsa daya na ke bashi, bana bukatar kudinsa," a cewar sa.

Mr. Iduoriyekemwen, wanda tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar dokoki ta jihar Edo, kuma daya tsohon mamba a hukumar bunkasa yankin Niger-Delta, ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya bayyana lambar wayar mamban kwamitin nasa, wanda ta hannunsa aka gabatar da cin hancin N1Om, don tabbatar da zarginsa.

A bangare daya kuwa, Shehu Sani, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bashi shawara kan harkokin siyasa, Suleiman Ahmed, ya ce wannan zargin an tsara shi ne kawai don bata sunan sanatan, musamman duba da takun sakar da ke tsakanin sanatan da gwamnatin jihar

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel