Alamu Sun Fara Tabbata, Gwamna Ya Gama Shirin Sauya Sheka daga PDP zuwa APC
- Alamu sun fara tabbatar da jita-jitar da ake yaɗawa cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na shirin sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
- Fitaccen mawakin nan, Davido ya yi wasu baituka a sabuwar waƙarsa da ke nuna gwamnan zai rungumi APC mai alamar tsintsiya
- Gwamna Adeleke da jam'iyyar APC sun sha musanta wannan jita-jita da cewa ƙarya ce da ba ta da tushe ballantana makama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya tabbatar da jita-jitar sauya sheƙar gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke daga PDP zuwa APC.
Davido ya bayyana alamun da ke nuna kawunsa, Gwamna Adeleke na shirin ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a sabuwar waƙarsa.

Source: Twitter
The Nation ta tattaro cewa tuni manyan ƙusoshi da masu ruwa tsakin PDP a jihar Osun suka fara sauya sheƙa zuwa APC, lamarin da ya sa ake ganin saura ƙiris gwamna ya biyo bayansu.

Kara karanta wannan
Sauya sheƙar Atiku ta rikita PDP da APC, tsofaffin gwamnoni da jiga jigai sun bi sahunsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jita-jitar sauya shekar gwamna ta yi ƙarfi
Jita-jitar sauya shekar Gwamna Adeleke ta fara karfi ne bayan ziyarar ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a lokacin bukukuwan babbar Sallah da ta gabata.
Gwamna Adeleke ya ziyarci Tinubu ne tare da Davido da ɗan’uwansa, Deji Adeleke, lamarin da ya haifar da zarge-zargen cewa yana shirin canza jam’iyya.
Sai dai, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Osun sun nuna rashin jin daɗi da yadda Gwamna Adeleke ke tafiyar da shirinsa na sauya sheƙa.
Tsohon sakataren APC na ƙasa kuma tsohon mataimakin gwamnan Osun, Sanata Iyiola Omisore, ya nuna damuwa kan yadda labarin canza shekar Adeleke ke yawo a soshiyal midiya kaɗai.
Tsohon saƙataren APC ya nuna damuwa
Da yake jawabi a shirin gidan talabijin na Channels TV a daren Talata, ya ce
"Ba zai yuwu a ce wani gwamna zai sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya amma ta kafafen sada zumunta kawai kake jin labarin ba."

Kara karanta wannan
'Za mu ci zabe cikin sauƙi': ADC ta fara harin gwamnan PDP da ke shirin shiga APC
"Kowace siyasa da kuke gani ana fara ta ne tun daga tushe, ban taɓa ganin gwamna yana matsa wa dole sai ya shiga jam'iyya ta sama ba."
Sanata Omisore ya ce shugabannin APC a Osun, dattawa da masu ruwa tsakin jam'iyya ba su da masaniya kan irin wannan shirin daga Gwamna Adeleke.

Source: Twitter
Davido ya tabbatar da shirin Gwamna Adeleke
Duk da cewa Adeleke da APC sun sha musanta wannan jita-jita a baya, wani ɗan gajeren bidiyon sabuwar waka da Davido ke shirin fitarwa ya ƙarfafa hasashen cewa gwamnan na shirin sauya sheƙa.
A cikin baitin waka, an ji Davido yana raira cewa “sabuwar tsinstiya za ta fi shara da kyau” da kuma “daga laima zuwa tsintsiya”, wanda ke nuni da tambarin APC (tsintsiya) da PDP (laima).
Duk da cewa bai ambaci sunayen jam’iyyun kai tsaye ba, kuma bai ambaci Adeleke ba a fili, ambatar tambarin jam’iyyun ya ƙara bayyana yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan Osun zuwa APC.
ADC na shirin amfani da sauyar shekar Gwamnan Osun
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ce sauya shekar Gwamna Ademola Adeleke daga PDP zuwa APC na iya ba ta damar lashe zaɓen gwamnan Osun.
Shugaban ADC na jihar Osun, Charles Omidiji, ya bayyana cewa idan har rahoton ya tabbata, to hakan zai iya ba jam'iyyarsa damar samun nasara cikin sauƙi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar haɗakar ADC ke shirin jawo gwamnonin jihohi biyar domin shirin tunkarar Bola Tinubu a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
