"Babu irin Buhari": Jigo a ADC Ya Gano Kalubalensu wajen Kifar da Tinubu a 2027

"Babu irin Buhari": Jigo a ADC Ya Gano Kalubalensu wajen Kifar da Tinubu a 2027

  • Salihu Lukman ya yi magana kan irin ƙalubalen da jagororin haɗaka za su iya fuskanta kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
  • Jigon na ADC ya bayyana cewa a cikin haɗaka babu mutum mai tasiri irin na tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari
  • Ya buƙaci ƴan haɗakar da su zama masu ƙanƙan da kai tare da gina ɗabi'ar yin aiki tare idan suna son samun nasarar kafa gwamnati a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mamba a cikin haɗakar jam’iyyun siyasa ƙarƙashin ADC, Salihu Lukman, ya yi magana kan tasirin Muhammadu Buhari.

Salihu Lukman ya bayyana cewa haɗakar ADC ba ta da wani mutum da ke da ƙima da tasiri irin na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Salihu Lukman ya yi magana kan hadakar ADC
Salihu Lukman ya ce babu mutum irin Buhari a hadaka Hoto: Salihu Lukman
Source: Facebook

Salihu Lukman ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Morning Show' na tashar Arise tv.

Kara karanta wannan

Bayan suka daga 'yan Arewa, Peter Obi ya fadi dalilin rashin zuwa jana'izar Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon ADC ya ba ƴan haɗaka shawara

Salihu Lukman ya shawarci mambobin haɗakar da su rungumi tawali’u tare da gina ƙwarin gwiwar aiki tare idan har suna fatan kayar da jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2027.

Ya kuma ce rasuwar Buhari na nuna ƙarshen wani zamani ne, wanda ɗaga hannun wani ɗan takara kawai ke nufin nasara kai tsaye a zaɓe.

Tsohon Shugaba Buhari dai ya yi tasiri sosai a siyasar Najeriya, inda yake da ɗumbin magoya baya.

Jigon na ADC ya ce tun kafin rasuwar Buhari, an riga an samu gibi a siyasar Najeriya. Ya ce kafin rasuwarsa ma akwai shakku ko Buhari har yanzu yana da tasiri wajen samar da nasara a zaɓe kamar baya.

“Abin da ya kamata mu koya, musamman a cikin haɗakar, shi ne babu wani da ke da irin girman suna da tasiri kamar marigayi Buhari."
"Kuma hakan na nufin dole ne shugabannin haɗakar su kasance masu tawali’u su gane cewa suna buƙatar juna."

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Matakin da APC ta dauka don karrama tsohon shugaban kasa

“Ba kawai batun kayar da APC da Tinubu ba ne, amma batun gina sabuwar ƙa’ida ta siyasa ce wacce za ta fara cika burikan ƴan Najeriya. Wannan ne nake maimaitawa akai-akai. Dole ne mu yi ƙoƙarin gina jam’iyyar siyasa mai ƙarfi.

- Salihu Lukman

Salihu Lukman ya tabo batun hadaka
Salihu Lukman ya ba 'yan hadaka shawara Hoto: Salihu Lukman
Source: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa (Arewa maso Yamma) ya ce daga yanzu ƴan siyasa dole ne su zama masu tawali’u, su cika alkawurran da suka yi yayin yaƙin neman zaɓe, kuma su kyautata dangantaka da al’umma.

Tsohon shugaban APC ya shiga jam'iyyar ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban APC mai mulki a Najeriya, John Odigie Oyegun, ya fice daga jam'iyyar.

John Oyegun ya tattara kayansa zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC bayan ya sanar da ficewarsa daga APC wacce ya taɓa shugabanta a baya.

Tsohon shugaban na APC ya zargi jam'iyyar da gazawa wajen share hawayen ƴan Najeriya tare da jefa su cikin halin yunwa da ƙaƙanikayi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng