'Yadda Aka Tono Wasiƙar Murabus Ɗin Atiku babu Izini Ana Alhinin Rasuwar Buhari'
- Hadimin Atiku Abubakar ya ce an tono wasikar murabus din mai gidansa daga jam’iyyar PDP ba tare da izini ba, aka yada a bainar jama’a
- Paul Ibe ya bayyana cewa wasu 'yan PDP da ke hada kai da APC ne suka fitar da wasikar domin su raunana Atiku, musamman a lokacin juyayi
- A cewarsa, kamata ya yi a maida hankalikan mutuwar Buhari, ba wai rikicin siyasa ba, yana mai sukar ministan sufurin jiragen sama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Mai ba da shawara ga Atiku Abubakar kan harkokin yada labarai ya yi magana bayan murabus din mai gidansa.
Paul Ibe ya bayyana cewa an tono wasikar murabus din Atiku Abubakar daga PDP ba tare da izini ba inda ya soki wasu yan APC da PDP kan fitar wasikar.

Kara karanta wannan
"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu

Source: Twitter
Yayin wata hira da Arise News a daren Laraba 16 ga watan Yulin 2025, Ibe ya yi bayani kan cece-kuce da ke tattare da lokacin da wasikar ta bayyana a bainar jama’a.
Musabbabin murabus din Atiku daga PDP
Atiku ya aike da takardar murabus dinsa daga PDP a ranar 14 ga Yuli, 2025, zuwa shugaban jam’iyya na unguwarsu da ke Jihar Adamawa.
Daga baya, hadiminsa a kafafen sada zumunta ya wallafa wasikar, inda Atiku ya ce akwai “bambance-bambancen da ba za a sasanta su ba.”
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP ta kau daga manufofin da aka kafa ta akansu, abin da ya tilasta masa daukar wannan mataki.

Source: Twitter
Murabus din Atiku: An zargin 'yan APC, PDP
Paul ya ce wasu da ke kokarin hana Atiku Abubakar ci gaba da siyasa, ciki har da ’yan PDP da abokansu a APC ne suka fitar da wasikar murabus din.
Ibe ya kira wadanda suka fitar da wasikar da “baragurbin ’yan PDP da ke aiki tare da ’yan APC,” ya ce ya kamata a girmama Buhari yanzu, cewar The Nation.
Ibe ya ce:
"Wadanda ke cewa sun san dalilin murabus dinsa, shin su annabawa ne? Ya kamata mu tattauna wani batu ba wannan ba.
"Mun samu kanmu a wannan halin ne saboda wasu da ba su fatan alheri ga Atiku Abubakar suka tono wasikarsa. Eh, an tono ta.
"Abin takaici ne cewa ministan sufurin jiragen sama, wanda ya kamata ya fi mayar da hankali kan ayyukan jiragen sama, ya tsoma baki a lamarin."
Makinde ya magantu bayan murabus din Atiku
Kun ji cewa bayan Atiku Abubakar ya ɗauki matakin ficewa daga jam'iyyar PDP, hakan ya fara jawo hankulan gwamnoni a Najeriya wanda suka fara magana kan lamarin.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo shi ya fara magana inda ya bayyana cewa tafiyar Atiku ba za ta yi wa PDP illa ba, face ta ba ta damar warware wasu matsalolinta.
Makinde ya ce kowane ɗan siyasa na da ƴancin shiga PDP ko ya fita, amma duk wanda zai zama matsala gara ya yi tafiyarsa inda ya ce fitar Atiku babu abin da zai mata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
