Ana tsakiyar Jimamin Rasuwar Buhari, An Maka Shugaba Tinubu da Wasu Jiga Jigai a Kotu
- Yayin da gwamnati da ƴan Najeriya ke ci gaba da jimamin rasuwar Muhammadu Buhari, wasu lauyoyin sun maka Shugaba Bola Tinubu a kotu
- Lauyoyi masu gwagwarmayar kare muradun jama'a sun roƙi kotu ta umarci Shugaba Tinubu ya ayyana dokar-ta-ɓaci a jihar Zamfara
- Sun shigar da wannan ƙara ne sakamakon taɓarɓarewar tsaro da rikicin majalisar dokokin Zamfara musamman dakatar da mambobi 10
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Saboda damuwa da rashin tsaro da rikicin siyasa a jihar Zamfara, wasu lauyoyi masu fafutukar kare muradun jama’a sun shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Lauyoyin sun shigar da wannan ƙara ne domin neman kotun ta umurci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara.

Source: Facebook
Wadanda suka shigar da ƙarar su ne Reuben Boma (Esq.), Okoro Nwadiegwu (Esq.), da kuma Ƙungiyar One Love Foundation, kamar yadda Tribune ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu da jiga-jigan da aka shigar ƙara
Sun roƙi kotu ta tilasta Majalisar Tarayyar ta karɓi ragamar Majalisar Dokokin Zamfara saboda tabbatar da adalci, zaman lafiya, dimokuraɗiyya da ci gaban al’ummar jihar.
Wadanda lauyoyin suka shigar ƙara sune, Shugaba Tinubu, Ministan Shari’a na Tarayya, Kakakin Majalisar Wakilai, gwamnan Zamfara da kwamishinan shari'a na jihar.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1363/25 wacce aka shigar ta hannun babban lauya, Goddy Uche (SAN), sun gabatar da tambayoyi guda huɗu da suke so kotu ta tantance, tare da neman hukunci da bayyana matsaya a kansu.
A rahoton Leadership, sun nemi kotu ta tantance:
- Ko bisa tanade-tanaden sashe na 42, 92, 98, 100, 103, 104, 109 da 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da kuma halin da ake ciki na rikicin siyasa da na tsaro a Zamfara da majalisar dokokinta, ba za a iya ayyana dokar ta-baci ba?
- Ko bisa tsarin mulki, Shugaban Ƙasa na da ikon ayyana dokar ta-baci ta hanyar sanarwa, ba tare da sauke gwamna da mataimakinsa ba, kamar yadda Sashe na 305(1-3) ya tanada?
- Ko bisa Sassan 11(4) da 305 na tsarin mulki, dangane da kalubalen tsaro da rikicin Majalisar Dokokin Zamfara, musamman dakatar da mambobi 10 ba bisa ka’ida ba, hakan ba ya nufin ba za ta iya gudanar da aiki ba, kuma Majalisar Wakilai ta Tarayya ba za ta iya karɓar ayyukanta ba?
- Masu karar sun kuma nemi kotu ta bayyana cewa, duba da rikicin tsaro, rikicin al’umma da rikicin majalisa, hakan na nuni da rushewar doka da oda a jihar Zamfara da barazanar da hakan ke yi ga zaman lafiya da tsaro.

Source: Facebook
Buƙatun da lauyoyi suka nema a kotu
Daga cikin abubuwan da suka roƙi kotu ta yanke hukunci a kansu sun haɗa da:
- Umurni ga Shugaban Ƙasa da ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara, ta hanyar sanarwa, tare da aiwatar da duk wani iko da kundin mulki ya bashi a sashe na 305(2-3), ko da zai haɗa da sauke gwamna da mataimakinsa ko a'a.
- Bayani daga kotu cewa majalisar dokokin Zamfara ba ta da sahihanci na doka bayan dakatar da mambobi 10 ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya hana ta samun adadin da ake bukata domin gudanar da harkokinta.
- Umurni ga Majalisar Ƙasa ta tarayya da ta karɓi ragamar aikin majalisar dokokin Zamfara don kare zaman lafiya, adalci, dimokuraɗiyya da ci gaban jama’ar jihar da ƙasar gaba ɗaya.
Wane kuskure Shugaba Tinubu ya yi?
A wani labarin, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Abuja a Majalisar Dattawa, Ireti Kingibe ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya tafka kura-kurai a gwamnatinsa.
Ta ce daga cikin duk kura-kuran da shugaban ya yi, wanda ya fi muni shi ne naɗa Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.
Kingibe ta bayyana damuwarta kan yadda Wike ke ƙwace filayen da gwamnatin tarayya ta bai wa makarantu da muhimman wurare a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


