Ficewar Atiku Abubakar daga PDP Ta Girgiza Siyasar Najeriya, Gwamnoni Sun Fara Magana

Ficewar Atiku Abubakar daga PDP Ta Girgiza Siyasar Najeriya, Gwamnoni Sun Fara Magana

  • Matakin da Atiku Abubakar ya ɗauka na ficewa daga jam'iyyar PDP ya fara jawo hankulan gwamnoni a Najeriya
  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa tafiyar Atiku ba za ta yi wa PDP illa ba, face ta ba ta damar warware wasu matsalolinta
  • Makinde ya ce kowane ɗan siyasa na da ƴancin shiga PDP ko ya fita, amma duk wanda zai zama matsala gara ya yi tafiyarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar daga PDP a matsayin wata hanya ta ceto jam’iyyar daga rigingimun cikin gida.

Gwamna Makinde ya yi ikirarin cewa babu abin da tafiyar Atiku Abubakar zai ragi babbar jam'iyyar adawa da shi yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ficewa daga PDP: Lokuta 5 da Atiku ya sauya jam'iyya da dalilinsa

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamna Makinde ya ce tafiyar Atiku ba za ta yiwa PDP wata illa ba Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Makinde, ɗaya daga cikin gwamnonin PDP ya faɗi haka ne a bikin cika shekara 10 da nadin Oba Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi a matsayin Deji na Akure, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Atiku ya fice daga jam'iyyar PDP?

Atiku, ɗan takarar shugabancin ƙasa na PDP a zaɓen 2023, ya sanar da barin jam'iyyar a cikin wata wasiƙa mai ɗauke kwanan wata 14 ga Yuli, 2025.

Jagoran adawar ya aika wasiƙar zuwa ga shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Jada 1 da ke karamar hukumar Jada a jihar Adamawa.

A cikin wasiƙar, Atiku ya bayyana cewa PDP ta kauce daga tsarin da aka ginata akai, yana mai cewa ficewarsa abu ne mai raɗaɗi a gare shi.

Ficewar Atiku ta zo ne makonni bayan ya ƙulla ƙawance da wasu fitattun ’yan adawa da suka amince da jam’iyyar ADC a matsayin sabuwar mafita ta siyasa gabanin zaɓen 2027.

Gwamna Makinde ya mayar da martani

Kara karanta wannan

PDP ta yi babban rashi, tsohon ministan shari'a ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC

Da yake martani kan wannan ci gaban, Gwamna Makinde ya ce ficewar Atiku ba za ta rage karfin jam’iyyar PDP ko damar ta ba.

“Siyasa wasa ne na neman cika buri, kuma bana ganin ficewar Atiku a matsayin wata barazana ga PDP. PDP jam'iyya ce mai ƙarfi.
“Kana da ’yancin shiga da fita. Amma duk wanda zai hana PDP ci gaba, ya fi dacewa ya fice kawai.”

- Seyi Makinde.

Gwamna Makinde da Alhaji Atiku Abubakar.
Gwamna Makinde ya ce ADC va za ta iya dusashe farin jinin PDP ba Hoto: Seyi Makinde, @Atiku
Source: Twitter

Jam'iyyar ADC ta zama barazana ga PDP?

Makinde ya ce babu abin damuwa dangane da jam’iyyar haɗaka watau ADC, yana mai cewa ba wata barazana ba ce ga PDP, rahoton Punch.

"Bana ganin ADC a matsayin barazana ga PDP. Manufar dai ɗaya ce idan kana jin ba ka gamsu da irin tafiyar gwamnati ba, kana da ’yancin shiga kowace ƙungiya.”
“Gwamnoni za su zo su tafi, shugabannin ƙasa za su zo su tafi, amma ƙasarmu da jihohinta za su ci gaba da wanzuwa," inji shi.

Sule Lamido ya yi magana kan fita daga PDP

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce yana nan daram a PDP amma zai yi wa haɗakar ADC aiki a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

Sule Lamido ya bayyana cewa duk da yake yana marawa jam’iyyar ADC baya, ba zai gushe ba wajen yin biyayya ga PDP.

Tsohon gwamnan, wanda yana ɗaya daga cikin mutanen da suka kafa PDP, ya bayyana cewa haɗaƙar adawa ta shirya ceto ƴan Najeriya daga baƙin mulkin APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262