Ficewa daga PDP: Lokuta 5 da Atiku Ya Sauya Jam'iyya da Dalilinsa
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Atiku Abubakar ya sake raba gari da jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda ta kauce daga kan turbar da aka gina ta a kai
- A tarihin siyasar tsohon mataimakin shugaban ƙasan, ya sauya sheƙa har sau biyar daga jam'iyyu daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yana da tarihin sauya jam'iyya daga wannan zuwa wannan a tarihin siyasarsa.
Ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP a zaɓen 2023, ya tabbatar da yin murabus daga jam'iyyar.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP
Ficewarsa daga jam'iyyar PDP ya ƙara tabbatar da cewa siyasarsa za ta ɗauki wani sabon salo.

Kara karanta wannan
"An karya doka," Abin da Atiku ya yi ana jimamin rasuwar Buhari ya harzuƙa Ministan Tinubu
Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:
"A ganin da nake yi kan yadda jam’iyyar ke tafiya a halin yanzu wanda ya saɓa da tushen ƙa’idojin da muka gina jam’iyyar a kai, na ga dole na raba hanya da ita."
Lokutan da Atiku ya sauya sheƙa a siyasa
Wannan shi ne sabon sauyi a cikin jerin manyan sauya sheƙa da aka sha gani a siyasar Najeriya.
Jaridar The Punch ta duba manyan lokuta guda biyar da Atiku ya sauya jam’iyya tare da dalilan da suka sanya hakan:
1999: SDP zuwa PDP
A shekarar 1999, Atiku ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa ƙarƙashin PDP bayan ya sauya sheƙa daga SDP.
Sai dai, kafin a rantsar da shi, an zaɓe shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Olusegun Obasanjo, wanda daga bisani ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Atiku ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007.
2006: PDP zuwa AC
A shekarar 2006, Atiku ya fice daga PDP bayan saɓani da Shugaba Olusegun Obasanjo kan batun wanda zai gaje shi.

Kara karanta wannan
Ficewar Atiku Abubakar daga PDP ta girgiza siyasar Najeriya, gwamnoni sun fara magana
Ya koma jam’iyyar AC domin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2007, amma ya sha kashi a hannun Umaru Musa Yar’adua na PDP.
2009: Daga AC zuwa PDP
Bayan rashin jituwar siyasa da jagoran AC a wancan lokacin, Bola Ahmed Tinubu, Atiku ya koma PDP a shekarar 2009.
Ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a 2011 amma ya yi rashin nasara, inda Goodluck Jonathan ya lashe tikitin.
2014: Daga PDP zuwa APC
A gabanin zaɓen 2015, Atiku ya fice daga PDP zuwa sabuwar jam’iyyar APC, inda ya zargi PDP da rashin dimokuraɗiyya a cikin gida.
Ya nemi ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC amma ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari, wanda daga baya ya kayar da Jonathan a babban zaɓe.
2017: Daga APC zuwa PDP
A shekarar 2017, Atiku ya sake komawa PDP, inda ya soki APC da gazawa wajen cika alƙawuran da ta ɗauka da kuma ware jiga-jigan jam’iyya.
Ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2019, amma ya yi rashin nasara a hannun Buhari.
2025: Daga PDP zuwa sabuwar jam'iyya
Atiku Abubakar ya sake tattara komatsansa daga jam'iyyar PDP a watan Yulin 2025.
Ya bayyana cewa ya fice daga PDP ne saboda kaucewa daga kan manufofin da aka kafa ta a kansu.
Ko da yake bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba tukuna, ana ganin cewa Atiku, zai koma jam'iyyar ADC.
Atiku tare da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark da sauran jagororin jam’iyyun adawa, sun amince da ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita wajen ƙalubalantar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Atiku ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu
A wani labarin kuma kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin mai girma Bola Tinubu.
Atiku ya yi kalamai masu suka kan Tinubu kan yadda gwamnatinsa ta tsige tallafin man fetur.
Tsohon.mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cire tallafin ya jefa ƴaɓ Najeriya cikin halin yunwa da talauci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
