2027: Shugaban ADC Ya Fallasa Shirin Dakile Farin Jinin Jam'iyyar
- Muƙaddashin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ya yi zargi kan gwamnatin jam'iyyar APC
- David Mark ya nuna cewa akwai shirin da gwamnatin za ta yi domin ganin ta dusashe tauraruwar ADC wadda ke haskawa a halin yanzu
- Kalamansa na zuwa ne bayan an samu wasu lauyoyi da suka shirya kare jam'iyyar a kowace shari'a a faɗin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban riƙo na ƙasa na jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, ya nuna yatsa kan gwamnatin jam'iyyar APC.
Sanata David Mark ya yi zargin cewa gwamnatin APC na shirin amfani da kotuna don kawu cikas ga tashen da ADC ke yi.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce ya yi wannan gargaɗin ne a birnin Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar lauyoyin ADC na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abdurrahman.

Kara karanta wannan
ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyoyi sun shirya kare ADC
A yayin taron, Abdullahi Abdurrahman ya bayyana cewa aƙalla lauyoyi 310 ne suka bayar da kansu domin kare jam’iyyar a duk wasu shari’u da ake yi ko za a fuskanta a nan gaba a faɗin Najeriya.
Ya ce tawagar lauyoyin ADC tana da wakilai a dukkan jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, kuma an tanadi duk abin da ya kamata domin fuskantar kowane irin ƙalubalen shari’a da jam’iyyar za ta iya fuskanta.
Ƙungiyar lauyoyin jam’iyyar ADC na ɗauke da fitattun masu shari’a kamar Barrista Peter Oyewole (shugaban ɓangaren shari’a na jam’iyyar), tsohon ministan shari’a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami (SAN), da kuma tsohon gwamnan jihar Edo kuma masanin shari’a, Farfesa Oserheimen Osunbor.
"Mun shirya tsaf don kare jam’iyyar ADC a duk inda wata shari’a ta taso a faɗin ƙasar nan."
- Abdullahi Abdulrahman
Ya ƙara da cewa lauyoyin sun yi amanna kan ƙwarewar shugabancin jam’iyyar na yanzu da kuma burin da take da shi na kawo sauyi mai amfani ga cigaban ƙasa.
David Mark ya nuna damuwa kan ADC
A nasa jawabin, Sanata David Mark ya bayyana damuwa kan yiwuwar samun barazana ta fuskar shari’a.

Source: Twitter
"ADC ita ce jam’iyyar da za a yi gogayya da ita a 2027. Gwamnatin yanzu na iya ƙoƙarin amfani da kotu don rage tasirinmu"
- Sanata David Mark
Ya roƙi ƴan Najeriya da su mara wa jam’iyyar ADC baya a matsayin wani zaɓi wanda sauya alƙiblar ƙasar nan.
Sanata David Mark ya kuma yaba wa lauyoyin jam’iyyar bisa ƙoƙarinsu da sadaukarwarsu, inda ya ƙarfafa su da su kasance a ankare da himma yayin da jam’iyyar ke shirin zama babbar mai neman mulki a babban zaɓe na gaba.
Al-Mustapha ya faɗi matsayarsa kan ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya yi magana kan jam'iyyar ADC.
Al-Mustapha ya caccaki jagororin haɗaka waɗanda suke son kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa ba zai shiga cikin haɗaka ba saboda bai gamsu da mutanen da ke cikinta ba.
Asali: Legit.ng
