'Na Gano Kuskure a Haɗakar Atiku, El Rufai': Al Mustapha Ya Faɗi Matsayarsa kan ADC
- Tsohon dogarin Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya ce ba zai shiga hadakar siyasa ba saboda rashin gaskiya da ruɗani
- Ya ce wasu daga cikin 'yan hadakar suna yaudarar juna, suna kokarin kawar da abokan tafiyarsu domin su zama jagorori su kaɗai
- Al-Mustapha ya zargi wasu daga cikin shugabannin hadakar da kasancewa cikin masu mulkin baya da suka jefa Najeriya cikin kunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon mai tsaron marigayi Janar Sani Abacha ya yi magana kan dambarwar siyasar Najeriya.
Manjo Hamza Al-Mustapha ya caccaki masu shirin haɗaka domin tunkarar zaben 2027 da ke tafe a Najeriya.

Source: Facebook
Hamza Al-Mustapha ya fadi dalilin kin shiga haɗaka
Al-Mustapha ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar DCL Hausa wanda aka wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin hirar, Al-Mustapha ya bayyana manyan dalilai da ya sa ba zai shiga jam'iyyar haɗaka da ADC ba.
A cewarsa:
"Tun da aka fara maganar farko ni na fara cewa bana cikin hadaka, tun da aka fara haɗaka ai sai ka tsaya ka yi lissafin mutanen da ka gani.
"Duk lokacin da ka ga ana taro sai ka ga taron bera da kyanwa ne to komin dadewa dai ka san ba zai tafi daidai ba.
"Watakila su yan hadakar ba su fadawa mutane gaskiya, idan sun hadu suna maganar kawar da APC."

Source: Facebook
Al-Mustapha ya fadi matsalolin hadakar ADC
Al-Mustapha ya kuma bayyana irin cin dunduniya da su kansu masu shirin haɗakar ke yi wa juna a bayan ido.
"Amma idan suka rabu suka koma tsakaninsu da masoyansu suna ta kokarin ya za a yi su kawar da sauran yan haɗaka su wuce gaba, to wane irin yaudara ne wannan, ya aka yi haɗaka ta zama haɗaka?."

Kara karanta wannan
A ƙarshe, Garba Shehu ya yi magana kan batun sa wa Buhari 'guba' a AC lokacin mulkinsa
"Ni na yi imanin zan yi wani abu ko ban shiga haɗaka ba, waɗanda suke tare da ni fa? Ko wadanda nake tare da su? Jam'iyya ta fa da sauran kungiyoyi da suke tare da ni fa?
"Wadanda suka yi hadakar nan fa sun yi mulki jiya mutane sun gansu sun san halayyarsu kuma kowa idonsa ya waye, wannan wata sabuwar Najeriya ce da ke cikin ukuba da kuma zafi.
"Idan har za a ce ga haɗaka an yi sai kuma aka kawo wasu mutane da suka kawo gurbata jiya saboda kawar da wani gurbatacce, to me aka yi kenan."
Al-Mustapha zai tsaya takarar shugaban kasa
Kun ji cewa Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin Sani Abacha, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 a ƙarƙashin SDP.
Ya bayyana wannan kuduri a Minna, inda ya jaddada aniyarsa ta yi wa Najeriya hidima da dawo da martabarta idan ya samu shugabanci.
Shugaban SDP na Neja, Buhari Yakubu Yarima, ya yi maraba da kudurin Al-Mustapha, yana mai fatan jam'iyyar za ta karbi mulki a 2027.
Asali: Legit.ng
