'Yadda Sunan Mahifainmu Ke Hana Mu Samun Alfarma': Zainab Buba Galadima
- Zainab Buba Galadima ta ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta ba ta wata dama, kuma ba ta taba zuwa neman kwangila tun hawansa mulki ba
- Ta bayyana cewa mahaifinsu Buba Galadima bai taba nema musu alfarma ba, kuma suna fuskantar takura saboda suna ganin mahaifinta na sukar gwamnati
- Zainab ta kara da cewa a lokacin Muhammadu Buhari ta yi aiki ba tare da albashi ba, amma an hana ta dama saboda cewar mahaifinta na sukar gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Yar siyasa Zainab Buba Galadima ta sake yin magana kan mulkin Bola Tinubu a Najeriya.
Zainab Galadima ta fayyace gaskiya game da cewa gwamnatin Tinubu ta ba ta aiki inda ta ce ta yi aiki ba tare da albashi ba.

Source: Facebook
Zainab Galadima ta magantu kan gwamnatin Tibubu
Hakan na cikin wata hira da ta yi da DCL Hausa wanda aka wallafa a Facebook a daren jiya Alhamis 11 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin hirar, Zainab Galadima ta fadi yadda sunan mahaifinsu ke dakile su samun wasu damarmaki a Najeriya.
Ta ce mahaifin nasu bai taba nema musu alfarma ba domin su samu wani abu a rayuwarsu.
Ta ce:
"Tun da shugaba Tinubu ya hau, ban taba zuwa na nemi kwangila ba, kaman a lokacin Muhammadu Buhari babanmu yana korafi sosai lokacin ina aiki a Villa.
"Aiki ma da nake a wurin ba albashi nake dauka ba, suna gani na babu yadda za su yi da ni suna tsoron korata a yi magana.

Source: Twitter
'Yadda na yi aiki ba albashi' - Zainab
Zainab ta kuma bayyana yadda ta yi aiki a fadar shugaban kasa ba tare da ana biyanta ko sisin kwabo ba amma ana ta tsangwamarta.
Ta bayyana cewa an sha fada mata cewa ba za a taimake ta ba tun da babanta yana zagin gwamnati ba kakkautawa.
Zainab ta kara da cewa:
"Amma aka barni kuma ba albashi ake biya na ba, kuma idan na je neman alfarma ba a yi mani.
"Wasu ma suna fada ta yaya za mu taimake ki bayan babanki yana zaginmu, duk an fada ka da ku taimake ta ai babanta yana zaginmu."
Zainab ta ce Buba Galadima ya taba kiranta lokacin da Muhammadu Buhari ya ci mulki inda ya ke yi mata nasiha kan rayuwa.
Ta bayyana cewa ya gargade ta cewa ka da ta yi tunanin tana da ilimi ko kusanci da Buhari idan lokacinta bai yi ba, ba za ta samu abin da take so ba.
Zainab Galadima ta caccaki Bola Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Zainab Buba Galadima ta ce Bola Tinubu zai fuskanci gagarumin kalubale daga Arewacin Najeriya a zaben 2027.
Ta ce watakila shugaba Bola Tinubu ba zai samu fiye da kashi 30 na kuri’un Arewa ba saboda rashin gamsuwa.
Zainab ta bayyana cewa haɗakar ‘yan adawa da ƙin jin daɗin jama’a na nuna cewa wannan zabe zai fi na 2023 wahala.
Asali: Legit.ng

