A kaf APC babu wanda yayi irin kokarin da ‘Diyata tayi – Buba Galadima

A kaf APC babu wanda yayi irin kokarin da ‘Diyata tayi – Buba Galadima

- Injiniya Buba Galadima yace Yarinyar sa ta fi kowa ilmi a Gwamnatin Buhari

- Buba Galadima yace ‘Diyar cikin ta sa ta bada gagarumar gudumuwa a APC

- Wannan ya sa yake ganin ba laifi bane don tana aiki a cikin Gwamnati mai ci

A kaf APC babu wanda yayi irin kokarin da ‘Diyata tayi – Buba Galadima

Zainab Buba Galadima tana da digiri birjik fiye da kowa inji Mahaifin ta
Source: Facebook

Tsohon sakataren jam’iyyar CPC wanda ta shige cikin tafiyar APC, Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa Yarinyar da ya haifa a Duniya, wanda ta ke tare da shugaba Buhari, ta fi kowa ilmi a cikin gwamnatin nan ta APC.

Dattijon yayi hira da BBC Hausa a makon nan inda ya bada amsa game da tambayar da ake yawan yi masa a game da ‘diyar cikin sa da ke aiki a fadar shugaban kasa duk da cewa yana cikin manyan ‘yan adawar Buhari a Najeriya.

KU KARANTA: Buba Galadima ya fadi abin da ya sa yake yakar Shugaba Buhari

Alhaji Buba Galadima yake cewa hidimar da ‘diyar nan ta sa tayi a tafiyar APC kafin a kafa gwamnati, ya fi karfin gudumuwar da shi kan sa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ba shugaba Muhammadu Buhari.

Galadima wanda yake tare da Atiku yanzu yake cewa a lokacin da APC ta ke kokarin kafa gwamnati, diyar sa tana rike da mukami. A wancan lokaci dai har shi kan sa Buhari bai rike da wani mukami a Najeriya inji Galadima.

Kakakin na yakin neman takarar Atiku Abubakar a PDP ya bayyana cewa bayan mukamin da yarinyar ta sa ta rike, tana da Digiri na farko har 2, sannan kuma tayi karatun digirgir har ta samu shaida 3, kuma yanzu haka ta koma aji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel