2027: Shekarau, Amaechi da Jerin Tsofaffin Gwamnoni da Ministoci da Suka Shiga ADC
- Manyan jiga-jigan siyasa a Najeriya sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC, inda suka kafa hadakar adawa mai karfi gabanin zaben 2027
- ADC na ci gaba da karbuwa a Najeriya yayin da rahotanni ke nuna cewa wasu gwamnoni da ministoci suna dab da sauya sheka zuwa jam'iyyar
- A wannan rahoton mun jero tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni da suka shiga ADC domin kalubalantar AP da PDP a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Ana ci gaba da samun gagarumin sauyin fasalin siyasa a Najeriya, yayin da manyan jiga-jigan siyasa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Wannan alama ce karara cewa ADC ta dauki mikatin zama wata babbar rundunar 'yan adawa da ba a taba gani ba gabanin babban zaben 2027.

Source: Facebook
Tsofaffin ministocin Buhari sun ce sai ADC
A sahun gaba cikin waɗanda suka sauya sheka akwai tsofaffin ministocin gwamnatin Muhammadu Buhari da suka hada da:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Rotimi Amaechi (Tsohon ministan sufuri)
- Abubakar Malami (Tsohon ministan shari'a)
- Rauf Aregbesola (Tsohon ministan harkokin cikin gida)
- Hadi Sirika (Tsohon ministan sufurin jiragen sama)
Wadannan jiga-jigan, wadanda suka kasance ginshikai a mulkin APC, sun bayyana kin amincewarsu da tafiyar jam’iyyar, suna mai cewa lokaci ya yi da za a kafa sabuwar jam’iyya mai gaskiya da ma’ana ga al’umma.
Masana na ganin sauya shekar na wadannan tsofaffin ministoci a matsayin babban sauyi da ke iya sauya taswirar siyasar Najeriya, inda suka taru a inuwa daya domin kalubalantar APC da ma PDP.
David Mark da haduwar tsofaffin gwamnoni a ADC
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, wanda ya shafe shekaru a jam’iyyar PDP, ya zama shugaban riko na ADC tun a watan Mayu.
A gefe guda kuma, Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan Osun shi ne ke rike da mukamin sakataren ADC na kasa, wanda ke nuna cewa jam’iyyar na kokarin hada kwararru don tunkarar 2027.
Daga cikin wadanda suka kafa kawancen 'yan adawa akwai tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda yake aiki kafada-da-kafa da Atiku Abubakar a ADC.
John Odigie-Oyegun, tsohon gwamnan Edo da kuma shugaban farko na APC, shi ma ya sauya sheka zuwa ADC – lamarin da ke jawo hankula, inji rahoton Vanguard.
A matsayin daya daga cikin waɗanda suka gina APC tun 2015, ficewarsa daga jam’iyyar na nuna rashin gamsuwa da yadda lamura ke tafiya yanzu.
A matakin jihohi, Ahmed Mahmud Gumel, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, ya zama kwamishinan ADC na jiha.
Duk da cewa Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na 2023 kuma tsohon gwamnan Anambra, bai yi rajista da ADC a hukumance ba, amma ya halarci taron kaddamar da jam'iyyar.
Hakazalika, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da kungiyarsa sun shiga hadakar kawancensu Atiku da kuma jam'iyyar ADC.
Akwai kuma rahoton da ya nuna cewa tsofaffin gwamnonin jihohin Benue, Cross River da Jigawa – Gabriel Suswam, Liyel Imoke, da Sule Lamido suna cikin tattaunawa don shiga hadakar ADC, ko su goyi bayanta a bayan fage.

Kara karanta wannan
Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

Source: Facebook
Tasirin ADC a siyasar Najeriya gabanin 2027
A cewar majiyoyin daga ADC, gwamnonin jihohi biyar da tsoffin ministoci 14 suna a matakin karshe na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Har yanzu dai ana ci gaba da boye sunayensu, domin dalilan dabarun siyasa yayin da ake tattaunawa da su a sirrance.
Wannan sabon ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da talauci, rashin tsaro da gajiya da mulkin APC ke kara tasirin a tsakanin 'yan Najeriya.
Ko da yake akwai shakku a wasu sassa game da dorewar wannan hadaka, amma kowa ya amince cewa ADC na samun karbuwa a halin yanzu.
Yanzu haka, zaɓen 2027 na kara daukar zafi, inda hadakar ADC ke karɓar manyan jiga-jigan siyasa, kuma idan har aka ci gaba da haka, jam’iyyar na iya zama wadda za ta sauya alkiblar siyasar Najeriya gaba ɗaya.
'Atiku ta zama jam'iyyar doke APC a 2027'
Tun da fari, mun ruwaito cewa, kawancen masu adawa da gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar sun amince da ADC a matsayin jam'iyyar hadaka gabanin zaɓen 2027.
An naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark matsayin shugaban ADC na ƙasa, yayin da Rauf Aregbesola ya zama sakatare, sai kuma Bolaji Abdullahi a matsayin kakakin jam’iyyar.
Manyan jiga-jigan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai sun bayyana kwarin guiwar cewa ADC za ta iya doke APC da Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng


