2027: Gwamna Dauda Lawal Ya Cika Baki kan Sake Yin Takara da Matawalle

2027: Gwamna Dauda Lawal Ya Cika Baki kan Sake Yin Takara da Matawalle

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kalamai kan magabacinsa kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle
  • Dauda Lawal ya yi addu'ar Allah ya sa Matawalle ya zama ɗan takarar APC a 2027, domin cikin sauƙi zai sake kayar da shi
  • Hakazalika, ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar PDP inda ya musanta jita-jitar shirin komawa APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi magana kan sake fafatawa da Bello Matawalle a zaɓen 2027.

Gwamna Dauda Lawal ya ce yana da tabbacin cewa zai sake kayar da Bello Matawalle kafin ƙarfe 10:00 na safe a ranar zaɓe.

Gwamna Dauda ya cika baki kan Matawalle
Gwamna Dauda ya ce da wuri zai kayar da Matawalle a 2027 Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels tv a ranar Laraba, 9 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Lawal ya yi magana kan yiwuwar ya sauya sheka zuwa jam'iyyar haɗaka ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dauda ya musanta shirin komawa APC

Hakazalika ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Ya tabbatar da cewa yana nan daram a PDP, yana mai cewa babu wani shiri ko niyya da yake da shi na ficewa daga jam’iyyar.

"Har yanzu ina cikin PDP, kuma ban da wani shiri na barin jam’iyyar a yanzu."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa kira da matsin lamba daga APC da wasu ƙungiyoyin siyasa suna yi ne don neman karkatar da hankalinsa kawai.

Ya jaddada cewa irin waɗannan ƙoƙarin ba su hana shi nasara ba a zaɓen 2023.

"Lokacin da na tsaya takara a 2023, duk waɗannan masu tasiri suna can, Sani Yerima, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Abdulaziz Yari, Matawalle, dukkansu suna cikin APC, amma na ci. Ba na jin tsoron su a 2027. Allah ne yake ba da mulki."

Kara karanta wannan

Moro: Babban sanatan PDP a majalisa ya tsage gaskiya kan shiga hadaka

- Gwamna Dauda Lawal

Me Gwamna Dauda ya ce kan Matawalle?

Yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke nuna cewa Matawalle, wanda yanzu haka shi ne ƙaramin ministan tsaro, yana shirin yin takara, Dauda Lawal ya ce yana maraba da ƙalubalen.

Hakazalika ya bayyana cewa ba ya kallon Matawalle a matsayin wanda zai kawo barazana ga siyasarsa.

Dauda Lawal ya yi kurari kan Matawalle
Dauda Lawal ya ce Matawalle ba barazana ba ne a gare shi Hoto: Dauda Lawal, Dr. Bello Matawalle
Source: Facebook
"Ina roƙon Allah ya sa Matawalle ya zama ɗan takarar APC a zaɓen 2027. Za mu ga abin da zai faru. Zuwa ƙarfe 10:00 na safe a ranar zaɓe, komai ya kammala, InshaAllah."
"Ba na ganinsa a matsayin barazana ko kadan. Ban damu da shi da har hakan zai sa na rasa bacci ba."

- Gwamna Dauda Lawal

Ya ƙara da cewa babu wani abu da ya canza tun bayan zaɓen da ya wuce wanda zai bai wa tsohon gwamnan fifiko.

ADC na zawarcin Gwamna Dauda Lawal

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ƴan haɗaka, ta fara zawarcin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.

Kara karanta wannan

Haɗakarsu Atiku ta ƙara ƙarfi, jam'iyyar ADC ta yi babban kamu a jihar Ƙatsina

Shugaban jam'iyyar na jihar Zamfara, Kabiru Garba, ya tura saƙon gayyata ga Gwamna Dauda domin ya shigo ADC.

Ya bayyana cewa sun gayyaci gwamnan ne zuwa jam'iyyar ADC domin kawo ci gaba a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng