An Fara: Hadimin Ganduje Ya Ce za Su Rama abin da Tinubu Ya Musu

An Fara: Hadimin Ganduje Ya Ce za Su Rama abin da Tinubu Ya Musu

  • Hadimin Abdullahi Ganduje, Aminu Dahiru Ahmad ya ce shugaba Bola Tinubu ya yi wa ‘yan APC na Kano abubuwa uku marasa dadi
  • Ya ce Ganduje ne ya fito da APC daga rikici har ya mayar da jam’iyyar ta zama mai karfi da tasiri a duk fadin Najeriya
  • Dahiru ya bayyana manyan nasarori da Ganduje ya samu a matsayinsa na shugaban APC da suka hada da sauya shekar manyan ‘yan siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hadimin tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna rashin jin dadi game da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hadimin mai suna Aminu Dahiru Ahmad ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘yan jam’iyyar da ke Kano rauni sau uku.

Kara karanta wannan

'Ya yi masa halacci': An fadi alakar Buhari da Tinubu bayan zargin sabani

Hadimin Ganduje ya ce Tinubu ya musu rauni sau 3
Hadimin Ganduje ya ce Tinubu ya musu rauni sau 3. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Aminu ya fadi haka ne a wani sako da ya fitar a Facebook, inda ya nuna cewa Tinubu bai nuna godiya ga kokarin Ganduje ba, duk da irin gudummawar da ya bayar wajen farfado da APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ranar da za a gane cewa Abdullahi Ganduje ne gatan APC na nan tafe kuma za su rama abin da aka musu.

A cewar shi:

"Yan APCn Kano Tinubu ya mana rauni sau daya sau biyu har sau uku. Allah ya kai mu ranar ramuwa, ranar da za su gane Ganduje ne rufin asirinsu."

Aminu ya ce Ganduje ya ceto APC

A cewar Aminu Dahiru, Ganduje ya karbi ragamar jam’iyyar APC a lokacin da take cikin rikici, bayan zaben 2023 da ya bar jam’iyyar da rabuwar kai a matakin kasa da jihohi.

Aminiya ta wallafa cewa Aminu ya ce Ganduje ya yi yawo jihohi domin sasanta 'yan APC, ya hade bangarori, ya kuma mayar da jam’iyyar tsintsiya madaurinki daya.

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

Yadda Ganduje ya jawo mutane APC

Aminu ya ce jam’iyyar APC ta samu karbuwar manyan ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyu a karkashin shugabancin Ganduje, ciki har da gwamnonin jihohin Delta da Akwa Ibom.

Ya ce har tsohon mataimakin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Ifeanyi Okowa ya sauya sheka tare da dukkannin magoya bayansa zuwa APC karkashin Ganduje.

Hadimin Ganduje da ya yi wa Tinubu korafi.
Hadimin Ganduje da ya yi wa Tinubu korafi. Hoto: Aminu Dahiru Ahmad
Source: Facebook

Tasirin Ganduje a Arewa da Kudu

Hadimin ya ce a Kano, Ganduje ya jawo fitattun ‘yan siyasa kamar Kawu Sumaila, Rurum, Dr. Baffa Bichi da sauransu, wadanda suka bar NNPP suka koma APC.

Ya kara da cewa a Kebbi kuwa, Sanatoci uku daga PDP sun sauya sheka zuwa APC a gaban Ganduje, wanda hakan ya kara wa jam’iyyar karfi da shahara a Arewacin Najeriya.

A cewar shi, a karkashin Ganduje ne jam’iyyar ta kafa cibiyar The Progressive Institute domin kara wayar da kan matasa da shirya tsare-tsare na bunkasa shugabanci mai nagarta.

Kara karanta wannan

'Barci ba naka ba ne,' Malamin addini ya zaburar da Tinubu kan haɗakar ADC

'Yar Buba Galadima ta tsorata Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Zainab Buba Galadima ta gargadi shugaba Bola Tinubu kan zaben 2027 mai zuwa.

Zainab Buba Galadima ta ce akwai alamun 'yan Arewa da dama ba za su zabi shugaba Bola Tinubu ba.

Ta bukaci 'yan APC da shi kan shi shugaban kasar su tashi tsaye domin ganin masu hadaka a ADC ba su kayar da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng