2027: Jagora a Jam'iyyar ADC Ya Fadi Dalilinsu na Son Raba Tinubu da Mulki

2027: Jagora a Jam'iyyar ADC Ya Fadi Dalilinsu na Son Raba Tinubu da Mulki

  • Tsohon Minista a zamanin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung ya fadi manufar ADC na son karbar mulki daga APC
  • Ya ce yan Najeriya sun gaji da azabar da su ke sha, musamman ta fuskar matsin tattalin arziki da ke ci wa jama'a tuwo a ƙwarya
  • Dalung, ya kuma musanta zargin da ake yi na cewa tsofaffin yan siyasa ne kawai su ka cika ADC don su cika burin kansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Tsohon ministan matasa da wasanni kuma jigo a ADC, Solomon Dalung, ya ce babu wani daga cikin shugabannin jam’iyyar da ke da niyyar neman shugabanci don muradin kansa.

Dalung ya ce tsantsar kishin ƙasa da kuma ƙudurinsu na ceto Najeriya daga halin da ya ce gwamnatin jam'iyyar APC ta jefa ƙasar ne ya sa suka yunkuro domin kawo agaji.

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

Solomon Dalung, tsohon Minista a gwamnatin Buhari
Solomon Dalung ya ce ADC za ta taimaki talaka Hoto: Solomon Dalung
Source: Facebook

A wata tattaunawa da Nigerian Tribune, Dalung ya bayyana cewa yawancin ‘yan Najeriya sun gaji da salon mulkin jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya Kara da cewa wasu daga cikin abubuwan da ya damu jama'a shi ne halin matsin tattalin arziƙi da tabarbarewar tsaro da ƙasar ke ciki.

Jagoran ADC ya ce 'yan Najeriya sun gaji

Solomon Dalung ya ce waɗannan matsaloli ne suka sa mutane ke neman mafita, kuma yanzu sun fara kallon ADC a matsayin madadin da za su dogara da ita.

Yayin da yake jawabi a garin Jos ranar Litinin, Dalung ya ce:

“Har zuwa inda na sani, babu wani daga cikin manyan shugabannin ADC da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.
"Idan har akwai, wajibi ne su kira taron manema labarai su bayyana hakan a hukumance."

Dalung ya yi bayanin manufar ADC

Dalung ya ce muradin da wasu 'yan ADC ke da shi na mulkar Najeriya a 2027 ya samo asali ne daga kishin kasa da burin samar da jagoranci nagari.

Kara karanta wannan

"Ba a kama shugaban ADC yana cusa daloli a aljihu ba," Dalung ya wanke ƴan APC tas

Dalung na ganin wannan zai haɗa kan al’umma da gyara tsarin tattalin arzikin da ke tangal-tangal a halin yanzu.

A kalamansa:

“Muradin ceto ƙasa da gina ta ba za a kira shi da mummunan ƙuduri ba, domin abin da ya cancanta a kira da mummunan buri shi ne wanda ya dogara da son zuciya da muradin ƙashin kai.”
Solomon Dalung ya ce talaka ya gaji
Dalung ya ce jama'a sun fara neman sauki Hoto: Solomon Dalung
Source: Facebook

Dalung ya musanta cewa wasu daga cikin jagororin ADC na ƙoƙarin sake dawo wa mulki ne don su ci gaba da muzgunawa talaka.

Ya ce su masu kishin ƙasa ne, waɗanda suka nuna damuwa da yadda abubuwa ke tabarbarewa a mulkin APC.

An shawarci ADC kan tsayar da dan takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa Yusuf Datti Baba-Ahmed, abokin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi a zaben 2023, ya yi kira ga ADC kan tsayar da Atiku Abubakar takara.

Wannan furuci na Datti na zuwa ne bayan an fara hasashen ADC na iya tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takararta a 2027.

Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi gargadin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da APC sun riga sun san dabarun siyasar Atiku, kuma sun riga sun kayar da shi a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng