ADC: Shafin Hadakarsu Atiku Ya Samu Matsala sau 3 a Mako 1, An Bayyana Dalili
- Shafin yanar gizon ADC ya fuskanci matsala sau uku sakamakon yawan masu shiga domin yin rajistar zama sababbin mambobin jam'iyyar
- Ibrahim Mani, shugaban kwamitin BoT na ADC ya ce sau uku suna gyara shafin a makon jiya, wanda ya ce hakan ya nuna ana kaunar jam'iyyar
- Jam'iyyar ADC na da burin zama babbar jam'iyyar adawa a Najeriya yayin da jiga-jiganta irinsu Atiku Abubakar ke burin cin zabe a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa shafinta na yanar gizo ya samu matsala sau uku a makon da ya gabata sakamakon yawan jama’ar da ke kokarin yin rajistar zama mambobinta.
Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT), Ibrahim Mani, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin.

Source: UGC
Shafin yanar gizon ADC ya samu matsala
Yayin tattaunawa da Channels TV, Ibrahim Mani ya ce yawan masu ziyartar shafin ya fi karfin tsarin da yake dauke da shi, lamarin da ya janyo ya samu matsala sau uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun dauki matakin sauya shafin yanar gizonmu sau uku a cikin mako guda saboda tururuwar masu son yin rajistar zama ’yan jam’iyyar ta hanyar intanet,”
- Inji Ibrahim Mani.
Legit Hausa ta fahimci cewa karuwar yawan masu ziyartar shafin ta biyo bayan bayyana ADC a matsayin sabuwar jam'iyyar hadakar ’yan adawa a Najeriya.
Fitattun jiga-jigan ’yan adawa ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na LP a 2023 Peter Obi, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola sun shiga jam'iyyar.
Abin da zai hana ADC ba dan siyasa tikiti
Ibrahim Mani ya jaddada kudurin jam’iyyar na gina babban dandalin ’yan adawa a kasar, tare da karbar sababbin mambobi da suka dace da manufofin ADC.
“Jam’iyyar siyasa gida ce ga kowa. Ba za a ce an ware wani mutum ba matukar ba wai kotu ta taba kama shi da aikata wani laifi ba.
"Domin kundin tsarin mulki ya haramta wa wanda kotu ta yankewa hukunci kan wani laifi shiga jam’iyya domin ya tsayawa takara."
- Ibrahim Mani.

Source: Twitter
Kokarin da ADC take yi gabanin zaben 2027
Jam'iyyar ADC na kokarin zama madadin jam’iyyun da ke da rinjaye a kasar ta hanyar hadin gwiwa da jiga-jigan 'yan Najeriya da kuma karfafa siyasa daga tushe.
Ibrahim Mani ya ce ’yan Najeriya na neman sauyi mai ma’ana musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki, wanda hakan ke karfafa sha’awa ga shiga jam’iyyar.
“Ya fi kyau a gina jam’iyyar da mutane masu kishin samar da sahihiyar adawa za su so shigarta fiye da barin Najeriya ta koma jam’iyya guda daya,” inji Ibrahim Mani.
Ya kuma ce jam’iyyar ADC na kokarin dawo da ayyuka zuwa yanar gizo yayin da ake ci gaba da wayar da kai ta hanyar tuntuɓar jama’a kai tsaye.
Tsohon minista, Adamu Waziri ya koma ADC

Kara karanta wannan
Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Adamu Waziri, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP kuma mamba a kwamitin amintattu (BoT), ya fice daga jam’iyyar, ya koma ADC.
Ya ce matakin ya biyo bayan damuwarsa kan halin ƙuncin da ’yan Najeriya ke ciki da kuma gazawar PDP wajen zama sahihiyar jam’iyyar adawa.
Waziri ya bayyana cewa ADC na da ƙarfin da za ta iya karɓe mulki daga hannun APC a 2027 domin dawo da martabar tattalin arziƙin ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

