"Gara Mu Faɗi Gaskiya," Ministan Jirage Ya Faɗi Gwamnan da Tinubu da APC Ke Tsoronsa gabanin 2027
- Festus Keyamo ya fito ya nuna cewa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana tsoron Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu saboda nasarorin da yake samu
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo SAN ne ya bayyana hakan yau Litinin, ya ce APC ta rasa hanyar da za ta bi ta kwace jihar Enugu
- Keyamo ya ce buƙaci Gwamna Mbah ya kula da kamfanin sufurin jiragen sama na Enugu Air, wanda aka kaddamar yau Litinin, 7 ga watan Yuli
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, a ranar Litinin ya yaba da irin nasarorin da Gwamnan Jihar Enugu, Dr Peter Mbah, ya samu.
Keyamo ya ce Gwamna Mbah yana daya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa kyakkyawan aiki a Najeriya, duk da kasancewarsa dan jam’iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan ƙera makamin nukiliya bayan yaƙin Iran da Isra'ila

Source: Facebook
Ministan ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da sabon kamfanin jirgin sama na Enugu Air a birnin Enugu yau Litinin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane gwamna ne Tinubu, APC ke tsoro?
Keyamo ya jinjina tare da yabon salon shugabanci da nasarorin da Gwamna Mbah ke samu tun da ya hau kan mulki a 2023 zuwa yau.
“Bari na maimaita abin da shugaban ƙasa ya ce kwanakin baya yayin kaddamar da wani aiki. Dr Peter Mbah, kai ɗan PDP ne, amma muna jin tsoronka.
"Hanyar da kake bi tana tayar mana da hankali, ba mu san yadda za mu tsara dabarar da za mu kayar da kai a zaɓe ba, amma muna kan shiri.
"Duk da bambancin jam’iyya, bai kamata mu ji tsoron faɗin gaskiya ba. Kana da burin ci gaba, ka yi abin a zo a gani a Jihar Enugu, kuma kana daga cikin gwamnoni mafi aiki.”
- Festus Keyamo.
Festus Keyamo ya ba Gwamna Mbah shawara
Keyamo ya kuma bukaci Gwamnatin Mbah ta tabbatar da cewa kamfanin Enugu Air ya kasance cikin tsarin kasuwanci mai inganci, ba tare da tsoma bakin siyasa ko tangarda daga ƴan siyasa ba.
A rahoton Channels tv, Keyamo ya ƙara da cewa:
"Abin da ya rage na shawara shi ne, kar a bar Enugu Air ya fada halin da tsohon kamfanin Nigerian Air ya fada.
"A tafiyar da shi da ƙwarewa, kada a bar siyasa ta hallaka Enugu Air. A tabbatar da cewa jirage na tashi da sauka akan lokaci.”

Source: Facebook
Kamfanin sufurin Enugu Air ya fara aiki
Kamfanin Enugu Air zai fara aiki da jirage guda uku na Embraer E170 da E190, wadanda aka zaɓa saboda sauƙin kula da su, jin daɗin fasinjoji, da dacewarsu da tafiye-tafiyen cikin ƙasa.
A ƙaron farko, jirgin zai fara jigilar fasinjoji daga Enugu zuwa jihohin Akwa Ibom, Abuja da Legas amma da yiwuwar a faɗaɗa shi zuwa Fatakwal, Owerro, Benin da Kano.
Bukola Saraki ya gana da gwamnan Enugu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya gana da Gwamna Peter Mbah da wasu jiga-jigan PDP a jihar Enugu.
Wannan taro wani ɓangare ne na ƙoƙarin da kwamitin da Saraki ke jagoranta domin farfaɗo da jam'iyyar PDP gabanin zaɓen 2027.
Saraki ya bayyana cewa sun tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka addabi jam’iyyar, tare da fara tsara sababbin matakai domin dawo da martabar PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

