Zaben 2027: Peter Obi Ya Fadi Tagomashin da Arewa Za Ta Samu idan Ya Yi Nasara
- Peter Obi wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya faɗi tanadin da ya yi wa yankin Arewacin Najeriya
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa yankin Arewa zai amfana idan ya zama shugaban ƙasa
- Ya bayyana cewa yana da shiri kan hanyar magance matsalolin rashin tsaro da suka daɗe suna ci wa yankin tuwo a ƙwarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Peter Obi, ya yi magana kan tagomashin da yankin Arewacin Najeriya zai samu idan ya hau kan madafun iko.
Peter Obi ya bayyana cewa yankin Arewa zai yi farin ciki da shi idan ya zama shugaban ƙasa.

Source: Twitter
Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar LP, kuma ɗaya daga cikin fitattun ƴan haɗakar adawa ya bayyana hakan ne a cikin shirin 'Sunday Politics' na Channels tv.

Kara karanta wannan
"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi yana da shiri kan Arewa
A cewarsa, babban arziƙin da Najeriya ke da shi yana cikin jihohi 19 na yankin Arewa, amma ba a amfana da wannan dama ba saboda matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
“Mun saba zaɓar rashin ƙwarewa, mun yi zaɓe bisa ƙabila, mun yi zaɓe bisa addini, yanzu lokaci ya yi da za mu zaɓi ƙwararru."
“Ina so su yarda da ni. Babban arzikin wannan ƙasa yana Arewa, gonakin da ba a noma ba. Zan magance matsalolin aikata laifi da muke fuskanta a Arewa a yau."
“Idan na zama shugaban ƙasa, Arewa za ta yi murna da ni. Ina da mafita kan matsalolin da ake fama da su."
- Peter Obi
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi alƙawarin zama shugaban ƙasa mai kulawa da jin ƙai.
Peter Obi ya caccaki Bola Tinubu
Ya zargi Shugaba Bola Tinubu da rashin nuna damuwa da halin da ƴan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan
Hanyoyi 7 masu sauƙi da za ka shiga jam'iyyar haɗaka ADC ko wata jam'iyya a Najeriya
Peter Obi ya ce Tinubu ya zaɓi yin hutu na Kirsimeti a Legas a watan Disamban 2024 maimakon ya kai ziyara Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda yara da dama suka mutu a cikin cinkoso a lokacin liyafar Kirsimeti.
“Babu tausayi, iyaye sun rasa ƴaƴansu waɗanda za su jagoranci ƙasar nan a gaba, amma ya tafi hutu na Kirsimeti."
- Peter Obi

Source: Twitter
Haka kuma, Obi ya soki Tinubu dangane da harin da aka kai a jihar Benue, inda ya ce ko da ya je Benue, bai je ƙauyen Yelwata ba, inda ake zargin makiyaya sun kashe mutane da dama tare da raba dubban mutane da muhallansu.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lalacewar hanyoyi da ambaliya ne suka hana shi zuwa wannan ƙauyen da bala’in ya fi shafa.
Peter Obi ya yabi Abdullahi Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya kwararo yabo ga tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Peter Obi ya yabi Ganduje ne bisa matakin da ya ɗauka na yin murabus daga kan muƙaminsa na shugabancin APC.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya buƙaci shugabanni da su riƙa yin koyi da Ganduje idan suka fahimci cewa ba su da lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng