PDP Ta Umarci Dukkannin Ƴaƴanta Su Shiga Sabuwar Jam'iyyarsu Atiku? Gaskiya Ta Fito

PDP Ta Umarci Dukkannin Ƴaƴanta Su Shiga Sabuwar Jam'iyyarsu Atiku? Gaskiya Ta Fito

  • PDP ta musanta rahoton da ke cewa ta umarci mambobinta su shiga sabuwar jam'iyyar haɗaka ta ADC da Atiku ya ƙaddamar
  • Kwamitin NWC na PDP ya bayyana a sarari cewa jam'iyyar ba ta ɗauki wani matsayi a hukumance kan batun haɗin kai ba tukuna
  • PDP tana mai da hankali kan warware barakar cikin gida da kuma shirye-shiryen Babban Taronta na Ƙasa don ƙwato mulki a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi magana game da rahotannin da ke yawo cewa ta umarci 'ya'yanta su shiga sabuwar jam'iyyar hadaka.

A jiya Laraba, Legit Hausa ta rahoto cewa su Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Peter Obi da sauran 'yan adawa sun kaddamar da ADC matsayin jam'iyyar hadaka.

Kara karanta wannan

Hadaka: Wike ya bar nuƙu nuƙu, ya fadi jam'iyya 1 da za ta iya rikita APC a 2027

Jam'iyyar PDP ta ce ba ta umarci mambobinta su shiga jam'iyyar hadakarsu Atiku ba
PDP ta karyata rade-raden daukar matsaya kan sabuwar jam'iyyarsu Atiku. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP ta nesanta kanta da hadakar adawa

A cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin PDP na X, Hon. Debo Ologunagba, sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa ya ce har yanzu ba su dauki matsaya kan hadakar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta nuna cewa rahotonnin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa ta umarci 'ya'yanta su shiga jam'iyyar hadaka ta ADC ba gaskiya ba ne.

Sanarwar Ologunagba ta ce:

"Hankalin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya kai kan wani rahoto da ke yawo a soshiyal midiya,wai PDP ta umurci mambobinta su shiga cikin jam'iyyar haɗaka.
"Don kauce wa ruɗani, NWC na sanar da 'ya'yanta cewa jam’iyyar PDP ba ta ɗauki wata matsaya a hukumance game da shiga wata haɗaka ba."

PDP ta mayar da hankali kan gina jam'iyya

Sanarwar ta ce yanzu PDP ta mayar da hankali ne wajen dinke duk wata barakar da take fuskanta, tare da hade kan 'ya'yanta.

Kara karanta wannan

ADC: Bayan hasashen El-Rufa'i, sabon rikici ya danno jam'iyyar hadakar adawa

Jam'iyyar ta ce tana so ta ga dawo da duk wani karfi da aka santa da shi, domin ba ta damar taka rawa matsayin babbar jam'iyyar adawa, da kuma kwato mulki a 2027.

Haka kuma, PDP ta ce hankalinta ya fi karkata kan yadda za ta gudanar da babban taronta na kasa, ba wai maganar shiga hadaka ba.

"Jam’iyyarmu a halin yanzu na aiki tukuru domin samun nasarar babban taron gangaminta na ƙasa, wanda zai ƙara farfaɗo da ingancin PDP domin fuskantar ƙalubalen da ke tafe."

- Debo Ologunagba.

PDP ta ce yanzu ta mayar da hankali kan dinke barakatarta da kuma shirya wa babban taronta na kasa
Sakataren watsa labarai na kasa, Hon. Debo Ologunagba. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Kofar PDP a bude take don doke APC a 2027

Duk da cewa ta nesanta kanta daga umartar 'ya'yanta su shiga jam'iyyarsu Atiku, PDP ta ce:

"A matsayinta na babbar jam’iyyar adawa mai cike da goyon bayan ‘yan Najeriya, PDP na sake jaddada cewa ƙofarta a buɗe take domin yin aiki tare dukkanin masu kishin ƙasa, a cikin yunƙurin ceto ƙasarmu daga halin ƙunci da ta shiga a karkashin gwamnatin APC."

PDP ta godewa ‘yan Najeriya bisa yadda suke nuna goyon baya ga jam’iyyar, tare da tabbatar musu cewa tana aiki tukuru don dawo da karfinta kafin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC: Tsohon dan takarar gwamna ya fice daga PDP a jihar Kano

Su Atiku sun zabi ADC matsayin jam'iyyar hadaka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar haɗakar 'yan adawa ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar ta zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar kalubalantar APC a zaɓen 2027.

An naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riko, tare da Rauf Aregbesola a matsayin sakataren riko, da Bolaji Abdullahi a matsayin kakakin yaɗa labarai.

Fitattun ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai sun bayyana ƙwarin guiwar cewa ADC za ta iya doke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com